Sauran Ma’aikatan Jami’a sun shiga yajin-aiki a kan tsarin IPPIS da kin biyan alawus

0
68

Kungiyar NASU ta ma’aikatan jami’an da ba su koyarwa a aji, sun bukaci ‘ya ‘yansu su tafi yajin-aiki da nufin jan-kunnen gwamnatin tarayya.

Jaridar Every day Belief ta fitar da rahoto cewa NASU ta ce mutanenta su dauke kafa daga zuwa ofis har na tsawon mako biyu daga ranar Litinin.

NASU ta fara wannan yajin-aiki ne a ranar 5 ga watan Oktoba, 2020, bisa zargin matsalolin da ake fuskanta daga manhajar biyan albashi na IPPIS.

Sauran Ma’aikatan Jami’a sun shiga yajin-aiki a kan tsarin IPPIS da kin biyan alawus

Wannan kungiya ta koka da cewa an ki biyan ma’aikatan jami’a bashin kudin da su ke bi daga karin albashin da aka yi a farkon shekarar nan.

Bugu da kari, NASU ta ce akwai wasu alawus da hakkokinta da gwamnati ta ki cika mata.

Kungiyar NASU wanda da farko ta goyi bayan shirin IPPIS, ta kuma ki zuwa yajin aiki, ta bi sahun takwararta ASUU wanda ta dade ta na yajin-aiki.

Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

Jaridar ta ce NASU ta na zargin akwai rashin gaskiya wajen yadda ake gudanar da sha’anin jami’o’in gwamnatin tarayya da ke fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar SSANU na kasa, Kwamred Samson Ugwoke, shi ma ya fitar da jawabi, ya ce ana cin zarafin sauran manyan ma’aikatan jami’a.

Samson Ugwoke ya na zargin malaman jami’a da yi masu ba-ba-ke-re a wajen aiki, abin da SSANU ta ce ya sabawa dokar da ta kafa jami’o’i.

Ba da dadewa ba ku ka ji cewa Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan wasu makarantu a Najeriya bayan lafawar annobar COVID-19.

Ministan ilmi ya ba duk wasu makarantu masu zaman kansu damar komawa bakin aiki.

What's On Your Mind?