Saukar Wannan Tsuntsun Zai Samar Da Zaman Lafiya A Borno

- Advertisement -

Daga Datti Assalafi.

Kamar yadda na karanta wannan labarin, ance Mutanen Borno Sun Fara Murnar Dawowar Zaman Lafiya: Zuwan Tsuntsaye Alamun samuwar zaman lafiya ne___ Manyan Dattijai.

An samu Bakuncin wani Babban Tsuntsu da ake kira Maiki ko Eagle a turance a jihar Borno.

Wasu Lattijai a jihar sun bayyana cewa Idan Barna, zalunci da cin hanci da Rashawa suka wanzu a bayan ƙasa Tsuntsaye Irin wadannan Shago, Angulu da sauran su, sukanyi ƙaura daga Irin wadannan wuraren, dawowar su kuma Alama ce ta samuwar zaman Lafiya da Adalci.

Shidai wannan Babban Tsuntsu an same shine a Maiduguri ya sauka a Shettima Baba Kura Kinandi’s Ajaganaram camp kusa da sabon Gidan Yari.

Ni kuma Datti Assalafiy a nawa fahimtar da kuma bincike, dawowar irin wadannan tsuntsaye masifa ne, dalili shine shi wannan tsuntsu yana cikin jinsin tsuntsaye ne wanda Malaman Biology suke kiran su da “Carnivorous birds” wato nau’in tsuntsaye da suke cin nama, bayan hatsi ko ciyawa da suke ci su rayu.

Bincike ya tabbatar da cewa irin wadannan jinsin tsuntsaye basa rayuwa sai a gurin da akwai nama, musamman tsuntsayen da basa iya kaiwa hari su kashe dabba su ci namanta, sun dogara ne akan naman da ya mutu, ko akaci aka bari.

Guraren da suke fama da matsala na yaki ko ta’addanci ana kisan rayuka, ana kashe mutane a zubar da gawarsu a jeji ba tare da an bunne ba, irin wadannan tsuntsaye su kan kaura zuwa gurin suna cin naman mutane da kuma dabbobin jeji da suka mutu a sanadiyyar gobarar daji.

Kasashen da akwai sahara ana samun wannan tsuntsaye, suna yawo a sararin samaniyar sahara suna neman gawarwakin mutane da dabbobin da suka mutu a sahara su ci namansu a matsayin abinci.

Don haka dawowar wannan tsuntsu kasar Borno ba alheri bane a nawa fahimtar, idan kuma akwai wasu masana da suke da nasu bincike akan wannan, su zo su kara bamu ilmi

Muna fatan Allah Ya kawo mana zaman lafiya a jihar Borno da Nigeria gaba daya Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

- Advertisement -