Sarkin Zazzau Ya Yaba Wa Malamai Da Suka Yi Tafsirin Azumi

- Advertisement -

Sarkin Zazzau Ya Yaba Wa Malamai Da Suka Yi Tafsirin Azumi

Daga Isa Abdullahi Gidan Bakko,

Mai martaba Sarkin Zazzau Jakada Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana matukar jin dadinsa ga malamai da suka yi tafsiri a watan azumin day a gabata, na yadda suka yi tafsirin day a hada kan al’umma da suka ilmantar da al’umma gudunmuwar da suka dace su bayar domin ciyar da kasa gaba ako wane fanni na rayuwa.

Sarkin ya bayyana batu ne a jawabinsa na bukukuwan sallah karama da ya gudana a masarautar Zazzau a jiya Alhamis.

Mai martaba Sarkin Zazzau ya kuma yi kira ga al’ummar masarautarsa da su yi amfani da wa’azin da suka ji, ta inganta yadda za su ci gaba da gudanar da rayuwarsu da ta gobe, ta yadda za su kuma san yadda za su ci gaba da bayar da gudunmuwarsu wajen ciyar da masarautar Zazzau da Nijeriya baki daya.

A dai jawabinsa mai martaba Sarkin Zazzau ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna na yadda gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a sassa daban na jihar Kaduna, wannan ayyukan ci gaba da gwamnati ta aiwatar, al’amari ne da al’ummar jihar Kaduna za su ci gaba da tuna wa da shi. A nan ne ya yi kira ga al’ummar jihar Kaduna, da su kula da ayyukan da gwamatin jihar ta aiwatar, domin kare ayyukan ‘yan baya ga dangi da suke lalata ayyukan ci gaba da gwamnati ta aiwatar.

Da kuma mai martaba ya juya ga batun tsaro, sai ya sake jinjina wa gwamatin jihar Kaduna, na yadda dare da rana gwamna da kansa ya ke sa ido kan batun tsaro da suka shafi garkuwa da mutane da kisar gilla da sauran matsalolin tsaro da suke addabar al’umma a daukacin kananan hukumomin jihar Kaduna 23.

Har ila yau, mai martaba Sarkin Zazzau ya jawo hankalin al’ummar masarautar Zazzau na su kara tashi tsaye wajen ba jami’an tsaro duk goyon bayan da suka ce tare da bayyana maboyan bata – gari, wanda zai iya zama silar yadda jami’an tsaro za su iya kwantar da ko wace irin matsala ta tsaro da ta ke addabar al’ummar masarautar Zazzau da jihar Kaduna da kuma Nijeriya baki daya.

A dai jawabinsa ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma jihohi da su ba manoma duk tallafin da suke bukata, domin su sami damar gudanar da noman da suka noticed a gaba a damuna mai zuwa, a cewar mai martaba Sarkin Zazzau, matukar gwamnatoci ba su tallafa wa manoma ba, za a iya samun matsalolin abinci da kuma sauran kayayyakin da al’umma ke amfani da su daga hannun manoma.

Tun farko a safiyar Alhamis da aka ambata, al’umma solar kasance a filin da ake kira filin Mallawa da ke kan hanyar Jos daga Zariya domin halartar sallar idi na farko daga zaben sabon sarkin Zazzau Jakada Ahmed Nuhu Bamalli, domin rabon da a yi sallar idi a wannan fili, an shafe fiye da shekara dari da suka gabata.

Tun kafin wannan rana ta sallah, majalisar masarautar Zazzau bisa jagorancin Chiroman Zazzau Alhaji Shehu Tijjani, ta gyara wannan fili tare das a duk wasu amsa – kuwa da za a yi amfani da su a ranar idin, kuma ga duk wanda ya lura da yadda aka gyara filin, babu wata matsala da aka samu a lokacin sallar idin da ta gabata.

Duk da masarautar Zazzau kwana daya kafin sallar idin, ta ce za a yi sallar idi karfe tara na secure, amma saboda jirar gwamnan jihar Kaduna, stated a aka kai karfe goma da minti ashirin da biyar, kafin babban Limamin Zazzau Sheikh Dalhat kasuim Imam ya tayar da sallah, a lokacin shi kuma sarkin Zazzau na zaune cikin mota, ya na jirar bayyanar gwamnan jihar Kaduna a wajen sallar idin da aka ambata.

Bayan kammala sallar idin ne, sai mai martaba sarkin Zazzau tare da daukacin Hakimai da aka zaba cewar su ne za su yi hawan karamar sallah suka hau dawaki zuwa kofar Doka zuwa Rimin Tsiwa zuwa Babban Dodo har dai zuwa fadar Zazzau, inda fadar ta yi cikar kwari na al’umma maza da mata da suka hallara domin gane idonsu hawan sallah na farko na sabon sarkin Zazzau, Jakada Ahmed Nuhu Bamalli.

Bikin Sallah a Zazzau ya sami halartar fitattun al’umma da suka hada dam asana ilimi da ‘yan siyasa da dai al’umma daban–daban.

 

- Advertisement -