Sarkin Karaye Ya Amince Da Nadin Abba Chiroma Sabon Dagacin Rimin Gado

0
83

Sarkin Karaye Ya Amince Da Nadin Abba Chiroma Sabon Dagacin Rimin Gado

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II bayan gamsuwa da zabin da al’ummar Garin Rimin Gado Suka yi wa Abba Ibrahim Chiroma, ya tabbatar da nadinsa a matsayin Dagacin Rimin Gado da ke Jihar Kano.

 

Sarkin ya amince da nadi Abba Chiroma bayan zabarsa da wadanda suke da alhakin zabar Sarakuna na Karamar Hukumar Rimin Gado auka gudanar ranar 14 ga watan March na shekara ta 2021.

 

Sabon dagacin ya gaji mahaifinsa Marigayi Alhaji Ibrahim Yusif wanda ya rasu a watan Janairun Shekarar da muke ciki.

 

An haifeshi a Shekara ta 1968, basaraken na da shaidar ilimin koyarwa Mai zurfi (NCE) kanda har zuwa lokacin da aka nada shi a wannan matsayi ma’aikaci ne a Karamar Hukumar Bichi.

 

Sai da aka tabbatar da kwajin kwakwalwarsa domin kasancewa ba shida akaka da matsalar share shayen miyagun kwayoyi kamar yadda yake bisa dokar Hukumar dake yaki da sha tare da fataucin miyagun kwayoyi ta gindaya.

 

Da yake jawabi Jim kadan da kammala nadin, Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II ya bukaci sabon dagacin ya kasance mai biyayya ga hakiminsa da sauran Hukumomi.

 

Hakazalika Dakta Ibrahim Abubakar II ya horeshi da ya jagoranci al’ummar sa bisa gaskiya da adalci, sannan ya haneshi da hada Kai da masu aikata laifuka.

 

In one other debelopment, the Emir of Karaye Alhaji Dr Ibrahim Abubakar II has confirmed Malam Isah Audi and Isah Usman as Imam and Deputy Imam of Unguwar Zage-zagi Friday Moskue in Rogo native gobernment space.

 

A wani cigaban Kuma Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II ya amince da Malam Isa Audi da Isah Usman a matsayin liman da na’ibin Masallachin juma’a na unguwar Zage-Zagi Dake yankin Karamar Hukumar Rogo. Kamar yadda jami’in yada labaran Karamar Hukumar Karaye Haruna Gunduwawa, ya Shaidawa MOBILIZED9JA A Yau.

What's On Your Mind?