Sarkin Kano Da Sauran Fasinjoji Sun Tsallaka Siradin Hatsarin Jirgin Sama

- Advertisement -

Sarkin Kano Da Sauran Fasinjoji Sun Tsallaka Siradin Hatsarin Jirgin Sama

Daga Abdulrazak Yahuza Jere,

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran wasu fasinjoji da dama solar tsallaka siradin hatsarin jirgin sama na Kamfanin Max Air da ke jigila tsakanin Kano zuwa Abuja, bayan injin jirgin ya samu matsala kimanin minti 10 da tashi daga filin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Dama dai Jirgin mai lamba VM1645 da aka tsara ya tashi da misalin karfe 1:30 na rana, ya samu tsaikon karin minti 30.

An gano cewa bayan jirgin ya tashi da kimanin minti 10 ne sai ya fara tangadi a iska, kana daga bisani ya nemi yin saukar gaggawa.

Majiyoyi solar bayyana wa Day by day Nigeria cewa jirgin ya kusa yin hatsarin ne sakamakon matsalar da ya samu a cikin injinsa, yayin da wasu kuma suka dora alhakin faruwar lamarin da kutsen da wani tsuntsu ya yi wa jirgin.

Da yake bayyana yadda lamarin ya auku, daya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin, Dakta Samaila Suleiman ya ce abin da ya faru tamkar gargarar mutuwa ce, kana ya soki kamfanin jiragen da yin sakaci.

Dakta Suleiman ya ce suna cikin jirgin sai suka ji wata kara da ba su gane kanta ba lokacin da jirgin ya yi yunkurin tashi, kana ya yi fatali da batun ko abin ya auku ne dalilin wata matsala ta tsaro

“Na ji wata kara da ban gane kanta ba lokacin tashi amma sai na kauda kai. Na sha hawan jirgi a lokuta da dama amma ban taba jin irin wannan karar ba lokacin tashin jirgi.

“Matuka da ma’aikatan jirgin solar rasa ta yi saboda kamar jirgin ya kwace masu ne. Hatta irin sanarwar da ake yi din nan a cikin jirgi ba su yi ba har sai da muka tsinci kanmu a inda muka taso daga filin jirgi. Abin kamar gargarar mutuwa ce. Ni da wasu fasinjoji da dama mun shiga dimuwa. Yawancinmu mun fasa tafiyar muka koma gida.” In ji shi.

Duk kokarin jin ta bakin kamfanin na Max Air dai abin ya ci tura har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

 

 

- Advertisement -