Sarkin Gombe Ya Hori Musulmi Su Dabbaka Darussan Ramadan

- Advertisement -

Sarkin Gombe Ya Hori Musulmi Su Dabbaka Darussan Ramadan

Ya Jinjina Wa Gwamnatin Jiharsa Bisa Gudanar Da Kyawawan Ayyuka

 

Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmai da su ci gaba da dabbaka darusan watan na Ramadan wanda ke karfafa ibada da kyautata imani da Allah don ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Gombe da kasa baki daya, yana mai cewa har sai an lizimci hakan ne za a samu mafita daga dimbin kalubalen dake fuskantar kasar nan.

 

Sarkin na Gombe ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci tawagar sakuna da hakimai zuwa ga kai ziyarar barka da sallah wa gwamnan Gombe Muhammad Inuwa Yahaya a gidan gwamnatin jiyar shekaran jiya.

 

Mai Martaba Sarkin Gombe, Dakta Abubakar Shehu Abubakar na III, ya ce solar ziyarci gidan Gwamnatin ne don taya Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya murnar kammala azumin Ramadana cikin nasara da kuma yi masa gaisuwar sallah.

 

Ya kuma yi amfani da damar wajen jinjinawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa kyakkyawan matakin da ya dauka na magance matsalolin dake faruwa a jihar da kuma irin salon jagorancin sa na alheri wanda ya ce ya haifar da aiwatar da ayyukan raya kasa masu tasiri ga rayuwar al’umma musamman a karkashin shirinsa na gina hanyoyi masu tsawon kilomita dubu da dari daya don gina hanyoyi akalla kilomita dari-dari a kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomin jihar 11.

 

Ya kuma yaba wa gwamnan sosai a fannonin farfado da cibiyoyin kiwon lafiya, da sake farfado da bangaren ilimi; musamman; kwashe yara masu gararamba a kwararo zuwa makaranta, da biyan albashi akan kari da kuma biyan kudaden sallamar aiki wato giratuti ga wadanda suka yi ritaya da dai sauransu, yana mai bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a matsayin abin tarihi da ba a taba yin irin sa ba.

 

Ya lura cewa babu wani yanki a jihar da bai shaida irin ci gaban da gwamnatin jihar karkashin Gwamna Inuwa Yahaya ke samarwa ba.

 

A jawabinsa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya yi kira ga jama’ar Jihar Gombe su yi amfani da yanayin zaman lafiya da jihar ke da shi don shiga harkoki masu amfani kamar noma da kiwo da sana’o’i da kasuwanci don bunkasa tattalin arzikin su da cimma burukan su na kashin kai.

 

Gwamnan ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa shaida watan Ramadana wanda ya zo karshe da bikin Eid el-fitr da aka yi, yana mai kira ga Musulmai da wadanda ba Musulmi ba a jihar su kula da zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ya samu tushe a Gombe, wanda addinan Musulunci da Kiristanci suka koyar.

 

Sai ya baiwa al’ummar jihar tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen neman goyon baya, hadin kai da kyakkyawar shawara daga sarakunan da shugabannin al’umma don jagorantar jihar ta hanya mafi inganci da adalci. Ya kara da cewa nasarorin da ya samu cikin shekaru biyu na jagorancin sa bai samu ba sai da goyon bayan sarakuna da al’ummar jihar baki daya.

 

Gwamna Inuwa ya ce sai an samu zaman lafiya ne Gwamnati za ta iya samar da ababen extra rayuwa da sauran ayyukan ci gaba don jin dadin jama’a, don haka yayi kira ga jama’a su yi taka tsantsan tare da ririta zaman lafiyan da jihar ke da shi.

 

Da yake tsokaci kan shirin ci gaban Jihar Gombe na tsawon shekaru 10, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce idan aka samu nasarar aiwatar da shi yadda ya kamata, shirin zai haifar da ci gaba mai daurewa tare da bunkasa dukkannin fannonin rayuwa ta yadda jihar za ta zama matattarar masu zuba jari na cikin gida dana kasashen waje.

 

Recreation da damunar da ke kara shigowa kuwa, gwamnan ya shaidawa mahalarta taron cewa rahotanni da hasashen masana yanayi na nuni da cewa adadin ruwan sama da za a samu a bana zai fi yadda aka saba, saboda haka ya shawarci jama’a su tsabtace hanyoyin ruwa su kuma guji zubar da shara a magudanan ruwa don kiyaye aukuwar ambaliya.

 

Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba Gwamnatin Jihar zata fara aikin tsabtace hanyoyi da magudanun ruwa na musamman don baiwa ruwa damar kwarara ba tare da wata matsala ba. Ya ce gwamnatinsa tana aiki tukuru don magance matsalar kwarurruka da zaizayar kasa a jihar ta hanyar aiki da hukumar magance zaizayar kasa da alkinta ruwa ta Nijeriya NEWMAP.

 

Sai ya godewa Mai Martaba Sarkin na Gombe bisa wannar gaisuwa ta Sallah, yana mai baiwa uban kasar tabbacin himmatuwar gwamnatinsa na ci gaba da isar da romon dimokiradiyya ga jama’a a dukkannin lungu da sako na jihar kamar yadda ya alkawarta a yayin yakin neman zabensa.

 

Daga bisani Sarkin ya jagoranci dubatan mahaya dawakai masu ado cikin launuka iri daban-daban tare da gabatar da gagarumar fareti da caffa da ta kayatar don nuna girmamawa ga gwamnan da sauran manyan baki mahalarta.

- Advertisement -