Sanata Na’Allah Ya Bukaci NLC Ta Hada Kai Da Gwamnati A Kebbi

0
12

Daga Umar Faruk,

Sanata Bala Ibn Na’Allah mai wakiltar shiyyar Kebbi ta Kudu a majalisar Dattijai, ya yi bukaci kungiyar Kwadago a jihar Kebbi da ta hada kai da fahimtar juna dangane da gudanar da yajin aik a duk lokacin da bukatar hakan ya taso. Domin sulhu da kuma fahimtar tsakaninta da gwamnatin shi ne mafi alfanu ba gudanar da yajin aikin ba.

Saboda na san cewa jihar Kebbi na daya daga cikin jahohin kasar nan da ke da kyakyauwar alka da hulda ta aiki da kungiyoyin ma’aikatar da kuma masu zaman kansu.
Sanata Bala Ibn Na’Allah, yayi wannan kiran ne a wata a wani jawabi da ya fitar ta hannun mai bashi shawara kan harakokin yada labaru Alhaji Garba Muhammad a jiya da aka aikewa manema labaru a Birnin-Kebbi.

Sanata Na’Allah Ya Bukaci NLC Ta Hada Kai Da Gwamnati A Kebbi

Haka kuma sanatan ya yabawa da dattakon da shugabannin kungiyar Kwadago da TUC da suka nuna a jihar kan janye yajin aikin a cikin wuni daya.

Hakazalika ya ce, “kungiyar Kwadago ya kamata tayi la’akari da cewa jihar Kebbi na daga cikin jahohin kasar Nijeriya da matsaloli daban-daban da a ke fuskantar a Nijeriya.

Mun Shirin Yi Wa Mutum Miliyan Biyu Rijista A Adamawa – APC

“Saboda haka a wannan lokacin bai kama ta a ce kungiyar Kwadago ta jihar Kebbi ta shirya yajin aiki. A wannan lokacin yadace ace kungiyar ta Kwadago ta bada gudunmuwarta ga magance matsalolin da jama’ar jihar Kebbi ke fuskanta a matsayarmu na shuwagabannin da nauyi rarataya a wuyanmu, inji Sanata Bala Ibn Na’Allah.”

Bugu da kari ya nuna godiyarsa ga ma’aikatan gwamnatin jihar Kebbi kan irin goyon baya da suke bayarwa ga manufufin da kuma tsare-tsaren gwamnatin APC a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Daga karshe yana kara godewa dukkann masu ruwa da tsaki na jihar Kebbi kan nuna s damuwarsu na ganin cewa kungiyar Kwadago a jihar ta samu daidaito da gwamnatin domin maimakon ci gaba da gudanar da yajin aiki a jiharmu ta Kebbi.

What's On Your Mind?