(Hotuna) Sanata Goje ya angwance da hamshakiyar GMD ta kamfanin Binani, Hajiya Aminatu

0
101

Tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje a ranar Juma’a ya kara aure inda ya aura Hajiya Aminatu Dahiru Binani, a kasaitaccen biki da aka yi a babban birnin tarayya, Abuja.

Kasaitaccen bikin ya samu wakilcin shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, Gwamna Inuwa Abdulkadir na jihar Gombe, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ministan sadarwa Dr Isa Pantami, Sanata Gabriel Suswam, Abdullahi Adamu da Abdulmumin Jibrin.

Sanata Goje ya angwance da hamshakiyar GMD ta kamfanin Binani, Hajiya Aminatu

An fara daura auren da karfe 2:45 na yammaci yayin da tsofaffin gwAmanoni, Ministoci, sanatoci da ‘yan majalisar wakilai suka samu halarta.

A yayin jawabi a bikin, Gwamnan jihar Gombe, Abdulkadir, ya yi addu’a ga angon da dukkan jam’iyyar APC a jihar.

A wani labari na daban, kungiyar matasan arewacin Najeriya (CNNY), ta bukaci tsohon gwamnan jihar Abia, gwamna Orji Uzor Kalu ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2023.

Batun Wanda zai maye gurbin shugaban kasa Muhammad Buhari yana ta matsowa saboda saura shekaru 3 wa’adin mulkinsa ya cika.

Hakan zai bai wa ‘yan kudancin Najeriya damar fitar da gwaninsu. Jiga-jigan jam’iyyar APC irin su Asiwaju Bola Tinubu ne ake sa ran zasu amshi kujerar mulki da zarar wa’adin shugaba Buhari ya kare a 2023.

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

Hajiya Aminatu (Hotuna)

CNNY ta ce zasu rike wuta yadda Kalu, wanda yanzu haka sanata ne daga jihar Abia zai maye gurbin shugaban kasa a 2023.

CNNY solar sanar da hakan a wata takardarsu ta ranar 1 ga watan Oktoba, wadda shugaban su Zarewa Salisu Sageer da sakataren su na kasa, Abu Bature Dandume suka sa hannu.

An Bukaci Gwamna Buni Ya Gina Masana’antun Sarrafa Tumatir Da Shinkafa

Kamar yadda takardar tazo, “sakamakon zurfin tunani, yasa muke rokon mai girma tsohon gwamnan jihar Abia kuma bulalar majalisa, Sanata Orji Uzor Kalu ya zo yayi takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

“Mun amince dashi, sakamakon hangen nesansa, salon mulkinsa, jajircewarsa, mun yarda zai kawo wa Najeriya cigaba mai tarin yawa.”

What's On Your Mind?