Samun Jami’ar EDUSOKO Zai Taimaka Wajen Bunkasa Harkar Ilimi – Inji Gwamnan Neja

0
81

Samun Jami’ar EDUSOKO Zai Taimaka Wajen Bunkasa Harkar Ilimi – Inji Gwamnan Neja

Daga Muhammad Awwal Umar,

Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar samun jami’ar Edosoko na Bida zai taimaka wajen walwale samun gurabun karatun jami’a da jihar ke fuskanta.

Gwamnan ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakunci shugaban kwamitin amintattun jami’ar mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar da tawagarsa a gidan gwamnatin jihar.

Gwamnan yace akwai dalibai da dama da ke neman damar shiga jami’a, wanda ya tabbatar samun wannan jami’ar zai ba su damar cin ma wannan kudurin na su.

Gwamnan ya yabawa kwazon sarkin wajen tsayin daka da alkiblarsa na samun wannan jami’ar, yace da kwazon Etsu Nupe za a samu turbar samar da dalibai wadanda suka kammala karatun jami’a bisa kwarewa wanda ana bukatar masu ilimin da zasu ciyar da jihar gaba, inda ya bada tabbacin gwamnatinsa za ta goya baya dan cin ma wannan nasarar.

Shugaban kwamitin amintattun, mai martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, ya bayyana cewar ziyarar tasu dan su gabatarwa gwamnan takardar amincewar hukumar kula da jami’o’i ta kasa da aka amince dan fara karatun digiri a matsayin jami’a mai zaman kan ta a jihar.

Mambobin kwamitin gudanarwar jami’ar solar hada da Alhaji Dalhatu Aliyu Makama, ( Makaman Nupe), sai Farfesa Muhammad Alkali shugaban riko na jami’ar, Alhaji Aliyu Ndagi jami’in daga darajar jami’ar, da Injiniya Asian Imoke kwararren mai kula da tsarin jami’ar.

What's On Your Mind?