Samar Da Ruwan Sha: Al’ummar Lokoja Sun Jinjina Wa Karamar Ministar Abuja

0
93

Samar Da Ruwan Sha: Al’ummar Lokoja Sun Jinjina Wa Karamar Ministar Abuja

Daga Ahmed Muh’d Danasabe, Lokoja

Daya daga cikin manyan matsalolin da ke addabar mazauna birnin Lokoja da kewayenta shi ne matsanancin karancin ruwan sha wadda suka kwashe shakaru da dama suna fama da shi duk da cewa Lokoja ce mahadar manyan Kogunan nan biyu a Nijeriya, wato Kogin Neja da Binuwai ( Confluence of Riber Niger & Benuwai).
Gwamnatocin da suka shude, solar kasa kawo karshen matsalar karancin ruwan a birnin na Lokoja, koda yake tsohuwar gwamnatin PDP karkashin jagorancin gwamna Ibrahim Idris tayi iyakar bakin kokarinta na kawo karshen matsalar, inda ta gina katafaren gidan samar da ruwan sha a garin na Lokoja domin wadata al’ummar birnin da kewayenta da ruwa sha, amma duk da haka, lamarin ya gagari kundila.
Da yake ance mahakurci, mawadaci, sai gashi kwatsam a wannan karon, al’ummar garin na Lokoja da kewayenta solar samu dauki da taimako daga karamar ministar babban birnin tarayyar Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, wadda yar asalin karamar hukumar Lokoja ce.
Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu dai tayi hobbasa inda ta bada kwangilar samar da rijiyoyin burtsatsi irin na zamani a unguwanni daban daban dake garin na Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.
Unguwannin da suka ci gajiyar samar da ruwan shan solar hada da  mahadar Cinema( Cinema Junction dake gundumar Ward A da Unguwar Shabayagi dake gundumar Ward B da Unguwar Sarki( Palace) dake gundumar Ward C da kuma Unguwar Kura dake gundumar Ward D.
Sauran sune Unguwar Kabawa dake gundumar Ward E da babban masallacin Juma’a dake Lokoja da kuma sashin Kabawa- Kwakwa dake kan hanyar zuwa makabarta, duk a garin na Lokoja.
Wannan taimako na samar da ruwan sha da karamar ministar ta babbar birnin tarayyar Abuja tayiwa jama’ar garin Lokoja, ya faranta musu rai matuka gaya,lamarin da yasa suka rika tofa albarkacin bakinsu ta hanyar yaba mata, inda suke cewa, minista kam, ta gama musu komai.
Ahmed Abubakar Datti, wani matashin dan siyasa ne, wanda kuma yana daya daga cikin matasa masu fada aji a Unguwar Kura, wato daya daga cikin unguwannin da suka ci gajiyar samar da ruwan shan.
” A gaskiya, mu kan bamu da abinda zamu cewa Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, sai godiya.
Mun kwashe shakaru da dama, muna fama da matsalar karancin ruwan sha, sai gaji yanzu minista ta kawo  mana dauki, a don haka muke mika godiyarmu gare ta kuma muna rokon Allah ya biyata cikin taskarsa.
” Har ila yau, muna tabbatar mata da cewa, mu al’ummar Unguwar Kura,muna tare da ita a dukkan lamuranta. Allah ya taimaketa”Inji Ahmed Abubakar Datti.
Haka shima Alhaji Abbas dake Unguwar Sarkin Lokoja, cewa yayi, muna jinjinawa Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu a bisa hobbasawarta na kawo karshen matsalar karancin ruwan sha da al’ummomi dake Lokoja suka dade suna fuskanta.
Rashin isasshen ruwan sha yana daya daga cikin manyan matsalolin da muke fuskanta a nan birnin Lokoja, lamarin dake jefa jama’a cikin kuncin rayuwa.
” A saboda haka, muke yabawa minista sport da wannan taimako na samar mana da rijiyoyin burtsatsi irin na zama a unguwanni daban daban domin wadata mu da ruwan sha.
Allah ya saka mata da alheri, yasa ta gama lafiya”Inji Alhaji Abbas.
Wasu da basu so a ambaci sunayensu ba, suma solar yabawa Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu a bisa samarwa da jama’ar garin Lokoja da kewayenta tsaftataccen ruwan sha,sannan suka yi kira ga sauran masu rike da mukamai a gwamnati da kuma masu hannu da shuni da suyi koyi da karamar ministar ta babban birnin tarayyar Abuja, wato Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu.

What's On Your Mind?