Sakon Xi Jinping Ga Matasa

0
38

Sakon Xi Jinping Ga Matasa

Daga CRI Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha nanata cewa, idan har yara manyan gobe suna da manufofi da kwarewa da nauyi, hakika kasa tana da makoma da kuma fata.

Xi ya bayyana haka ne, a jaribirin ranar matasa ta wannan shekara, wadda ake bikinta Talatar nan, lokacin da daliban jami’ar Tsinghua suka marabce shi, a mtsayinsa na tsohon dalibin da ya kammala karatunsa a jami’ar. A lokacin ziyarar tasa, Xi Jinping, ya tsara wani kundin raya ilimi mai zurfi na kasar Sin da kara fatan da ya ke da shi kan dalibai matasa Ya kuma jaddada cewa, ya kamata matasa su rungumi buri da ake da shi a tarihi, su sa kaimi na zama jaruman sabon karni a matsayin muhimmin aiki na cimma burin farfado da kasa.

Xi ya kara da cewa, inganci da kokarin matasa, yana shafar matakan cimma mafarkin kasar Sin. Xi ya sha yiwa dalibai matasa bayani recreation da hanyar koyo, inda ya jaddada cewa, “Wajibi ne a koyi ilimi kamar yadda soso yake tsotse ruwa” domin karfafa ma’anar gaggawa a tsarin koyo.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?