Sakon Sallah: Kuji Tsoron Allah Ku Guji Zalunci –Inji Sheikh Aminu Sha’aban

- Advertisement -

Sakon Sallah: Kuji Tsoron Allah Ku Guji Zalunci –Inji Sheikh Aminu Sha’aban

Daga Ahmed Muhammed Danasabe,

An yi kira ga al’ummar musulmi dasu sanya tsoron Allah a dukkan al’amuransu na yau da kullum domin samun tsira a nan duniya da kuma can lahira.

Babban limamin garin Lokoja, Sheikh Muhammadu Aminu Sha’aban ne yayi kira a yayin da yake gabatar da hudubarsa kadan bayan ya jagoranci daruruwan al’ummar musulmi sallar Idi raka’a biyu, a babban masallacin Idi dake Felele, a garin Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, a jiya Alhamis.

Sheikh Aminu Sha’aban, wanda yace tsoron ne kawai mafita, ya kuma ce kowani mai rai zai bada ba’asin dukkan abubuwan daya aikata yana raye a ranan tashin Alkiyama.

Babban limamin ya kuma kara da cewa yin biyayya ga Allah tare da kaucewa aikata munanan ayyuka da kuma neman tuba daga Allah( SWT) ne kadai zasu kai ga dan Adam samun rahamar Ubangiji,yana mai jaddada cewa Allah( SWT) mai amsar tuba ne idan an roke shi gafara.

Sheikh Aminu Sha’aban ya kuma bukaci al’ummar musulmi,musamman masu hannu da shuni dasu rika bada sadaka da kuma fidda zakka kamar yadda Allah ya umurta.

Daga nan yayi addu’ar samun zaman lafiya ga jihar Kogi dama Nijeriya baki daya, musamman a wannan lokaci da kasa ke fuskantar barazanar tsoro.

Cikin wadanda suka halarci sallar Idin solar hada da mai martaba Sarkin Lokoja, Alhaji Muhammadu Kabir Maikarfi Na 111 da Wazirin Lokoja, Alhaji Abdulrahman Babakurun da Maiyakin Lokoja, Alhaji Ali Lawal Jiya da kuma sauran masu rawanin sarki.

- Advertisement -