Sake Farfado Da Borno: Engr Gubio Ya Ziyarci Aikin Rukunin Gidaje 1000 A Kaleri

0
113

Sake Farfado Da Borno: Engr Gubio Ya Ziyarci Aikin Rukunin Gidaje 1000 A Kaleri

A kokarin gwamnatin jihar Borno na samar da isassun gidajen da za a yi amfani dasu domin samar da muhalli tare da tsugunar da yan gudun hijira, kwamishina a ma’aikatar sake farfado da yankunan da rikicin Boko Haram ya shafa a jihar Borno (MRRR), Hon. Engr Mustapha Gubio ya kai ziyarar gani da ido ga aikin rukunin gidaje 1000 a Kaleri na karamar hukumar Jere a jihar, ranar Alhamis.

A lokacin da kwamishinan yake duba aikin rukunin gidajen, wanda ya hada da samar da ruwan sha, cibiyar kiwon lafiya, kasuwa tare da makaranta, ya bai wa yan kwangilar adadin makonni uku su tabbatar da kammala aikin gidajen.

Gwamnan Gombe Ya Nuna Takaicinsa Kan Masu Gina Gidajen Mai A Unguwanni

Bugu da kari kuma, wannan aikin rukunin gidajen yana daga cikin adadin gidaje 10,000 wadanda Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi alkawarin samar wa nan da karshen 2023 wanda aka shirya raba su ga yan gudun hijirar da za a mayar dasu yankunan su na asali.

Har wala yau kuma, Engr Gubio ya bai wa yan kwangilar tabbacin basu duk abinda suke da bukata wajen ganin solar kammala aikin a daidai lokacin da aka tsara.

What's On Your Mind?