Sai Mun Jajirce Wajen Tabbatar Da Nijeriya Dunkulalliyar Kasa – Obaseki

0
89

Sai Mun Jajirce Wajen Tabbatar Da Nijeriya Dunkulalliyar Kasa – Obaseki

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa sai ‘Yan Nijeriya mun jajirce musamman ma matasa wajen tabbatar da yin duk mai yiyuwa domin dorewar kasar a matsayin kasa daya dunkulalliya mai cike da hadin kai.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a karshen mako a filin wasanni na tunawa da Samuel Ogbemudia Stadium da ke Benin, babban birnin jihar, yayin da ya amshi ‘yan wasan tawagar Edo ‘Workforce Edo’ wadanda suka kammala fafatawa a gasar wasan kwallon kafa ta kasa (NSF), wanda jihar ta amshi bakwancin wasan da kuma suka zo na biyu a taka ledar da aka fafata.

‘Yan wasan da suka lashe kyautar zinare an baiwa kowannensu Naira 250,000, su kuma wadanda suka ci lambar azurfa an baiwa kowanne daga cikinsu Naira 100,000.

Gwamnan Edo na cewa: “Ba mu samu wani hatsarin da wani har ya sha magani ba. Matasan Jihar Edo solar nuna halaye na kwarai domin solar kauce wa shan kwayoyi a yayin gasar NSF, Edo 2020. Muna godiya ga dukkaninku. Mun yanke cewa bari mu hadu dukkaninmu domin mu ce da ku ‘Mun Gode’.

“Manufar samar da wasan NSF an kirkira ne a birnin Benin bayan yakin basasa, wanda shugabanin wancan lokacin suka amince kan cewa Nijeriya ta zauna a matsayin kasa daya al’umma daya, sai suka ga cewar akwai bukatar a samar da wani taron da matasan Nijeriya za su rika haduwa a wuri guda, dukka domin tabbatar da hadin kai.

“Allah ya albarkaci Nijeriya. Dole ne mu mika nagartacciyar kasa a hannunku (Matasa). Kada ku farrakata. Kada ku bari ta fada cikin rikici-rikicen da zai raba kan jama’a. kuna da abokai a dukkanin fadin kasar nan. abokanku da suke Arewa, Kudanci, Gabashi da Yammaci, shin solar kasance a wajenku kamar masu neman sauyi?.

“Kada ku fidda tsammani daga matsalar tsaro da ke faruwa a kasar nan yanzu. Fatanmu. Ku yi magana da babban murya domin tabbatar da Nijeriya ta kasance kasa daya, al’umma daya. Wannan shi ne sirrin da ke cikin gasar kwallon kafa na kasa da ake shiryawa NSF.”

Gwamna Obaseki ya nuna kwarin guiwarsa na cewa tabbas tawagar ‘yan wasan Edo za su yin kokari fiye da wanda suka yi a yanzu a yayin gasar taka ledar na gaba wanda zai gudana a jihar Delta da ke makwafta da su.

Shugaban karamin kwamitin shirya gasan Edo 2020, Philip Shaibu wanda kuma shine mataimakin gwamnan jihar Edo, ya jinjina wa gwamna Obaseki a bisa basu cikakken damar da sararin da suke bukata wanda ma hakan ne sirrin samun nasarorin da suka samu.

What's On Your Mind?