Safara’u ta bayyana dalilin da yasa aka dena ganinta a shirin ‘Kwana Casa’in’

0
133

Safara’u ta bayyana dalilin da yasa aka dena ganinta a shirin ‘Kwana Casa’in’

Safiyya Yusuf, jarumar Kannywood wacce ta yi fice saboda rawar da ta taka a cikin sanannen shirin talabijin mai suna ‘Kwana Casa’in’ da ake nuna wa kowanne mako a Arewa 24, Day by day Belief ta ruwaito.

Duk da kasancewarta daya daga cikin taurarin shirin da al’umma ke kauna sosai, an cire ta daga shirin ba tare da sanarwa ba. A hirar da ta yi da Weekend Journal, ta yi karin haske kan hakan da ma wasu abubuwa, ga wani sashi cikin abinda ta fadi.

A cewar Safiyya, “an maye gurbina ne da wata ne a shirin saboda ina ta fama da rashin lafiya sosai a wannan lokacin ake fim har ta kai bana iya zuwa wurin aiki”

Allah Sarki ! Rashida Mai Saa Tayiwa Marigayi Ibro Da Daushe Kyauta ta musamman

“An fara daukan sabbin shirin ban samu zuwa ba saboda rashin lafiyar don haka basu da wata zabi ila su maye gurbi na a wannan lokacin.”

Jarumar ta fara bayyana cewa ta fito ne a matsayin yarinya wacce ta dage ta yi karatu har da zama likita a shirin.

Mahaifiyarta na fama da matsanancin ciwon kafa don haka ta ke son ta zama likita don ta taimaka mata da ma wasu mutanen.

Kamar yadda majiyarmu ta samu daga Legit. A bangarensa mahaifinta shi kuma baya son ta da karatun, so kawai ta yi aure domin ya samu kudi daga manema auren.

Kazalika, ta ce tana yin wani shirin mai suna ‘Kaddarar So’.

What's On Your Mind?