Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja [Goto]

0
288

Sabon Katafaren Gidan Da Ɗan Uwan Buhari Ya Gina A Abuja

Dan majalisar wanda dan uwa ne ga Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci mutane su taya shi murna game da kammala ginin gidan.

– A cewar Fatuhu Mohammed, ya dauki kimanin tsawon shekaru hudu kafin kammala ginin dankareran gidan da yace a Gwarimpa Abuja ya gina.

Dan uwan Shugaba Muhammadu Buhari kuma dan majalisar wakilai na tarayya, Fatuhu Muhammed ya nuna sabuwar katafaren gidan da ya gina a Abuja, Legit hausa ta ruwaito.

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Gwamnan Benuwe

Mr Muhammed, wanda ke wakiltar mazabun Daura/Maiadua/Sandamu a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress APC, ya ce ya gina gidan ne a cikin shekaru hudu.

Dan majalisar ya nuna hotunan katafaren gidan alfarmar a shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya bukaci abokansa da masoya su taya shi da addu’ar nasarar abinda ya cimma.

Alhamdullilah, na kammala gina gida na a Gwarimpa (Abuja) da ya dauke ni kimanin shekaru hudu ginawa amma don haka dukkan godiya ta tabbata ga Allah kuma ina bukatar addu’o’in ku.

“Zan sanar da ranar tarewa a gidan nan gaba,” ya rubuta.

Jim kadan bayan wallafa sakon, dan majalisar ya cire hotuna da rubutun da ya wallafa.

What's On Your Mind?