Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji

0
43

Kungiyar masu tada kayar bayan Boko Haram a ranar Asabar ta saki sabon bidiyo dake nuna igwa, makamai da harsasan da mambobin kungiyar suka kwace a cikin dajin Sambisa, jihar Borno.

Daya daga cikin yan ta’addan wanda yayi jawabi a bidiyo mai tsawon mintuna 4.15 yayi jawabi kan artabun da sukayi da Sojojin a dajin Sambisa ranar Juma’a, HumAngle ta ruwaito.

Wata motar Igwa Vickers Mk.3 Eagle, harsasai igwa masu yawa da harsasan bindiga.

Wannan na faruwa a lokacin da dakarun Sojin Najeriya suka kaddamar da atisayen Operation Tura Takai Bango inda suka farautar yan ta’addan ISWAO a dajin Alagarno- yankin Timbuktu.

Sabon bidiyon Boko Haram ya nuna irin makaman da suka kwace hannun Soji

A wani labarin kuwa, mayakan Boko Haram a Nasarawa solar kashe sojoji tara a yayin wani aikin ceto a dajin da ke hanyar Mararaba-Udege a jihar Nasarawa wanda ke hada jihar da Otukpo Oweto a jihar Benue.

Yadda Ƴar fim Tayi Murnar Cika Shekaru 2 Ba Tare Da Yin Jima’i Ba

Sojojin da aka kashe wanda wani jami’i Felix Kura, dan asalin jihar Benuwe ya jagoranta zuwa dajin solar hada da Iliya Kefas, Bati Yakubu da wasu kananan jami’an da ba za a iya tantance sunayensu nan take ba.

Jaridar The Nation ta tattaro daga majiya cewa jami’an da aka kashe suna kan aikin fatattakar ‘yan ta’addan Boko Haram da suka sace yan asalin jihar da dama tare da tsare su daga dajin.

What's On Your Mind?