Saboda Rashin Tsaro… Nijeriya Na Iya Zama Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Da Marayu – Cibiyar Addinai

0
69

Saboda Rashin Tsaro…  Nijeriya Na Iya Zama Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Da Marayu – Cibiyar Addinai

Daga Abubakar Abba,

Cibiyar tabbatar da zaman lafiya da sulhu a tsakanin mabiya addinai a Nijeriya ta bayyana cewa matukar ba a dauki kwararan matakai na shawo kan matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan ba, kasar za ta iya zama sansanonin ‘yan gudun hijira da marayu saboda yawaitarsu da za a samu.

Har ila yau, ‘yan jarida da sauran mahalarta taron wallafa labaran zaman lafiya a Kaduna solar koka kan yadda al’amuran sace mutane da sauran nau’o’in matsalolin tsaro suka yi kamari a cikin watan Afirilun da ya gabata.

 

Taron wanda aka saba gudanar da shi a duk wata, Cibiyar Mabiya Addinai Mabanbanta wato Interfaith Mediation Middle ce take gudanar da shi bisa daukar nauyin Gidauniyra Mercy Corps.

 

Koken nasu na kunshe ne a cikin sanarawr bayan taron da Fasto Dakta James Mobel Wuye da kuma  Imam Dakta Muhammad Nurayn Ashafa wadanda dukkan su Daraktoci ne a Cibiyar suka rattaba wa hannu.

 

Solar kuma nuna takaicinsu kan yadda masu garkwar suka dauki sabon salon hallaka wadanda suka sace, in an samu jinkirin biyan su kudin fansa daga gun gwamnati ko gun iyayen wadanda suka sace.

Solar yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara daukar masu hali na gari aiki da za su yi aiki kafada da kafada da sauran jami’an tsaron kasar nan domin a yaki masu garkuwa da mutane a daukacin fadin kasar da kuma magance matsalar rashin tsaro da ke ci gaba da addabar Nijeriya.

 

Solar kuma yi kira ga wasu gwamnonin kasar nan, da su san irin kalaman da za su dinga furtawa kan abin da ya shafi garkuwa da mutane, domin gudun ka da su kara jefa rayuwar wadanda aka sace a cikin hadari.

Mahalarta taron solar kuma danganta karuwar rashin tsaro kan rashin ayyukan yi, inda suka yi nuni da cewa, hakan na kara sa masu garkuwa da mutane suke kara janyo musamman matasa a cikinsu.

 

Solar kuma koka kan yadda rikicin Fulani Makiyaya da Manoma ke kara kamari, musamman a jihar Binuwe.

 

Mahalart taron solar bayyana cewa, in har  mahukunta a kasar nan ba su dauki matakan gaggawa don magance matsalar rashin tsaro ba, Nijeriya za ta iya komawa fage na tara ‘yan gudun hijira da kuma marayu.

 

Solar bukaci matakan gwamnati uku da su samar wa da jami’an tsaro musamman sojoji da manyan makamai domin su tunkari ‘yan ta’adda da masu garkuwa yadda ya da ce.

 

Taron na wannan watan ya kuma samu halartar Jimi’an Cibiyar da suka fito daga jihohin Katsina, Binuwe, Filato, Kogi da kuma Kano.

What's On Your Mind?