Sa Biyar kaci Goma… Labari Mai Dauke Da Darasi A cikinsa Ga Tausayi Ga Dariya

0
33

Shahararen marubucin yanar gizo Malam Yasir Ramadan Gwale ya wallafa wannan rubutu a shafin wanda ga takaici ga dariya.

“Wani abokina na gani da carbi yana ja, gaskiya ban saba ganinsa da carbi ba, sai nake tambayarsa ko lafiya kuwa, ko wani ne ya mutu? Sai matarsa take shaida min cewar ai kudin sa ya saka a INSME wajen dubu dari biyar aka kwashe masa su. Shi ne fa ya rasa abin yi yake ta jan carbi.

Nace to wannan abin ashe haka ya yiwa mutane barna da yawa. Nayi masa jaje na kuma taya shi alhinin wannan asara. Sai yanzu nake ji ashe mutane da dama solar zura kudadensu a Uwork da Insme din nan, wasu kawai fuska suka yi suka ki fada, amma abin yana damunsu a zukatansu.

Sa Biyar kaci Goma… Labari Mai Dauke Da Darasi A cikinsa Ga Tausayi Ga Dariya

Yadda Bayan Saurayi na ya Gama Lalata Da Ni, yana Kawo Abokansa su Bashi ₦500 Su Ma suyi – Budurwa

Kamar dai yadda masu sharhi sukai ta bayani, wannan Sa biyar kaci goma din fa caca ce, amma mutane idonsu ya rufe kawai kudi suke so su samu a huce. Tsakani da Allah idan mutum yana da dubu dari biyar ko miliyan daya me zai kaishi yayi irin wannan gangancin na saka kudinsa a harkar da bai da cikakkiyar masaniyarta?

Me yasa mutane ba zasu koyi dabarun juya kudi da kansu sai solar bawa wasu da basu sani ba tare da tsammani za a kawo musu dukiyar da babu faduwa sai riba? Ai yanzu kasuwa ba sai ka bude shago ba, a gida zaku yi kai da matarka, kuna talla kuna samun masu bukatar kayanku kuna musu supply, amma mutane su gidadantar da kansu saboda suna son kudi cikin sauri.

Yana da kyau mutane su kiyaye da masu yi musu romon baka akan irin wannan abubuwa na damfara. Kuma ya dace mutane su koyi dabarun yin kasuwanci da kudade kadan ko da kuwa ta hanyar hadaka ne domin sarrafa ko samar da wani abu.

Wanda duk suka fada wannan tarko Allah ya kiyaye gaba, Allah ya mayar musu da alheri. Sannan a kiyaye gaba, domin kuwa irin wannan lamari yana nan birjik za ai ta fito da shi kala kala da salo iri iri ana ta jawabi amma duk na buge ne domin a yaudari mutane su zurara kudadensu. Allah ya kare.

Yasir Ramadan Gwale
31-01-2021
Kano.”

What's On Your Mind?