Rundunar ‘yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami’anta sun ci zarafin ka

Sashen kula da huldodin jama’a na rundunar ‘yan sandan Nigeria ya samar da lambobin waya da kafofin dandalin sada zumunta da WhatsApp domin tabbatar da tsaftataccen aiki a rundunar.

Rahotanni sun bayyana cewa, rundunar ta samar da wadannan hanyoyin ne domin yin nazari da sa ido ga ayyukan sashen FSARS da sauran jami’an kwantar da tarzoma da ke cikin ta.

Lambobin wayar da kafofin sadarwar an samar da su ne domin baiwa al’umar damar shigar da korafe korafe idan jami’an rundunar FSARS ko TS su ka ci zarafin su.

Rundunar 'yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami'anta sun ci zarafin ka

Lambobin aika sakon sune kamar haka:

Tawagar Sifeta Janar:

08036242591

FSARS:

08038537625

08036067446

08036059332

08069702133

Shigar da korafi ta kafofin sada zumunta:

Rundunar soji ta kakkaɓe ƴan bindiga a hanyar Abuja-Kaduna, ta ƙwato makamai (hoto)

07056792065 Kira/sakon SMS/whatsapp

08088450152 Kira/sakon SMS/whatsapp

E-mail: pressforabuja@police.gov.ng

Twitter: @PoliceNG

Shafin yanar gizo: www.fb.com/ngpolice

Sashen shigar da korafin gaggawa (CRU)

08057000001 – Kira zalla

08057000002 – Kira zalla

08057000003 – Sakon SMS & whatsapp kawai

Twitter: @PoliceNG_PCRRU

Mun ruwaito maku cewa, Sifeta janar na ‘yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma’aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da ‘yan Najeriya suke yi akan ‘yan sandam na zalunci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma’aikatan STS, IRT da kuma ACS.

An dakatar da ma’aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

Sakamakon rashin sanin makaman aiki irin na su kamar yadda a kan samu lauyoyi, ‘yan kasuwa, fastoci da sauran su suke yi.

Sannan shugaban ‘yan sandan ya dakatar da duk wani dan sanda da yin sintiri ko kuma wasu ayyukan ‘yan sanda da kayan gida, dole ne yanzu su dinga saka kayan aiki.

 232 total views,  1 views today

About M. Jamiu 1079 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*