Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar ‘yan ta’adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas

0
36

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata wani rahoton kafafen yada labarai na cewa ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas.

An bayyana rahoton a matsayin karya, na bogi, kuma mara tushe wanda aka tsara shi da nufin karya gwiwar jama’a da kuma karya lagon dakarun sojin a kokarin da suke yi wajen yaki da ta’addanci, jaridar The Nation ta ruwaito.

Mobilized9ja ta tattaro cewa kakakin rundunar soji, Birgediya Janar Mohammad Yerima ne ya fayyace gaskiyar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 11 ga Fabrairu, a Abuja.

A cewar Yerima, babu hari makamancin haka inda aka kashe sojoji 20, inda ya kara da cewa tawagar MSTs da tawagar bataliya 156 sun kakkabe harin da aka kaiwa dakarun.

Rundunar sojojin Najeriya ta karyata cewar 'yan ta'adda sun kashe sojoji 20 a arewa maso gabas

Bayan rashin nasarar aure har biyu Fati Muhd ta bayyana burin ta a duniya

Ya ci gaba da bayanin cewa tuni biyu daga cikin sojojin da suka samu raunuka suka fara karbar magani.

Jiragen Dakarun Sojojin Saman Nigeria, NAF, a ranar Laraba sun halaka yan bindiga masu yawa a mabuyarsu da ke dazukan jihar Kaduna, The Punch ta ruwaito.

Kwamishinan tsaron da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya lissafa wurarren da jiragen suka kai hari inda suka hada da Rahama, Tami, Sabon-Birni, Galadimawa da Ungwan Farinbatu.

Saura sun hada da Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon-Dawa, Ngade Allah, Kidandan da kuma wasu garuruwan da ke kananan hukumomin Birnin-Gwari da Giwa a jihar.

What's On Your Mind?