Boko Haram: Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sauran sabbin makamai na zamani

0
220
  • Har yanzu mayakan Boko Haram ba su daina kai hare-hare a kan farar hula da rundunar sojoji ba

  • Wasu daga cikin sojojin da ke yaki da ‘yan Boko Haram solar sha yin korafin cewa ba su makamai na zamani

  • Shugaban rundunar sojin kasa, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce solar karbin sabbin tankokin yaki da makamai na zamani

A ƙoƙarin da gwamnati ta ke yi wajen ganin ta magance matsalar tsaro da ƙasa ke fuskanta, rundunar sojin Najeriya ta kawo kayan yaƙi na zamani da sauran kayan yaƙe-yaƙe don gudanar da sumame a kan ƴan-ta’adda.

Shugaban rundunar sojin Najeriya,Tukur Buratai, ne ya bayyana hakan a yayin taron tattaunawa da sukayi a ranar talata a garin Maiduguri.

A cewar Buratai, wasu daga cikin makaman an siyo su ne daga ƙasar waje.

Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sauran sabbin makamai na zamani

Wasu kuma an kerasu ne a cikin gida ta hanyar aikin haɗin guiwa.

“Ya zuwa wannan lokaci, rundunar sojin mu ta kawo kayan aiki da zasu taimaka mata wajen yaƙe-yaƙenta.

“Kayan yaƙin solar haɗa da, tankokin yaƙi ƙirar VT4 da FT1, motoci masu gano abun fashewa da kuma bindigogi masu jigida dake sarrafa kansu ƙirar SH2 da SH5.

Ana nan ana gwajin waɗannan makamai kuma kwanan nan za’a ƙaddamar da su.

Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun sace mutum 18 a Kebbi

“Rundunar Sojin Najeriya ta karɓi motocin yaƙi masu sulke daga ƙasar Jordan kuma muna tsammanin ƙarin wasu makaman.

”A ɓangaren makamai na gida rundunar sojin Najeriya ta haɗa dirkokin yaƙi da motar gidigo,da kuma shingen yaƙi.

”Dukda ƙalubalen da muke fuskanta da sabbabbin makamai,wannan cigaba da aka samu ya ƙarawa sojojin mu himma da hazaƙa a fanni daban-daban.

”Za mu cigaba da aiki tuƙuru don ganin mu tallafawa kowane yaƙi da kayan aikin da ake buƙata”A cewarsa

Buratai ya jaddadawa kwamandoji bukatar su tabbatar an raba makaman bisa dai-daito don kada ayi asarar maƙudan kuɗaden da gwamnatin tarayya ta narka akansu.

Ya ce rundunar soji ta na samun gagarumar nasara a dukkan wani atisaye da suke gudanarwa a halin yanzu.

Shugaban rundunar sojin ya ƙara da cewa Sojoji na ƙoƙari wajen daƙile ayyukan ƴanta’adda, ma su tayar da ƙayar-baya,Ƴan bindiga daɗi, ma su garkuwa da mutane, ɓarayin shanu da kuma rikicin Manoma da makiyaya da sauransu.

Ya ƙara shaidawa kwamandojin da suke a filin-daga dasu tabbatar solar kawar da dukkan matsalar da ke barazana ga tsaro a faɗin ƙasa.

What's On Your Mind?