WATA SABUWA: Rikicin Siyasa Ya Barke A Jam’iyyar APC A Jahar Sokoto

0
148

Rikicin Siyasa Ya Barke A Jam’iyyar APC A Jahar Sokoto

A yau Lahadi, ya’yan jam’iyyar APC a jahar Sokoto sunci karo da wani faifan Bidiyo na kakakin majalisar dokoki ta jahar Sokoto Hon. Aminu Manya Achida yana gabatar da Dr Hon.Balarabe Salame dan majalisar tarayya mai wakiltar Gwadabawa da Illela a matsayin dan takarar Gwamna a zaben 2023 a wannan ta jam’iyyar APC.

A cikin bayanin Aminu Manya Achida, ya bayyana Hon. Abdullahi M Hassan tsohon Chiyaman na Sokoto ta Arewa a matsayin jiga-jigan wannan tafiya ta ganin an tsaida Hon. Balarabe Salame a matsayin dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC a zaben 2023.

Hotunan Dinner Nuhu Abdullahi (Mahmud Labarina) Da halartar Mawakan Kannywood

Aminu Manya Achida ya bayyana cewa “A tsarin siyasar jahar Sokoto idan akwai adalci a yanzu al’ummar Sokoto ta gabas ne yakamata ace dan takarar Gwamna ya fito daga yankinsu. Saboda haka solar shirya tsaf domin tsaida Dr Balarabe Salame a matsayin dan takarar Gwamna a jam’iyyar APC a zaben 2023”.

Sai dai akwai masu hasashen al’amurran siyasa dake kallon wannan a matsayin wata hanya ce da ake shirin tarwatsa jam’iyyar APC a jahar Sokoto tun kafin zaben 2023.

Yanzu dai ta tabbatar cewa Hon. Aminu Manya Achida da sauran wasu ya’yan wannan jam’iyya ta APC irinsu Abdullahi M Hassan solar 6alle daga tafiyar tsohon Gwamna Sanata Wamakko mai son ganin an sake tsaida Ahmad Aliyu.

Majiyarmu ta samu labari daga shafin sokototracker

What's On Your Mind?