Rikicin Kalifancin Tijjaniyya Ya Sake Kunno Kai A Nijeriya

- Advertisement -

Rikicin Kalifancin Tijjaniyya Ya Sake Kunno Kai A Nijeriya

Daga Abdullah Muhammad Sheka, Kano

 

Sheikh Mahi Ibrahim Inyass Ya Tabbatar Da Nadin Tsohon Sarki Sanusi II
Babu Irin Wannan Nadin A Tijjaniyya – Ibrahim dahiru Bauchi
Mun Yi Farin Ciki Da Nadin Domin Ya Gaji Kakansa – Shehi Shehi Mai Hula

Ga dukkan alamu rikici ya sake kunno kai a kan kalifancin darikar Tijjaniyya a Nijeriya wacce take da miliyoyin mabiya a sassan kasar, bayan an sanar da nadin tsohon Sarkin Kano mai martaba Sanusi Lamido Sanusi a matsayin sabon kalifa.
Babban Kalifan Tijjaniyya na duniya Sheikh Mahi Ibrahim Inyass ne ya tabbatar da nadin sabon kalifan a can kasar Senigal wanda nan ne shalkwatar ‘yan failar Tijjaniyyar.
Batun nadin sabon kalifan ya fara tasowa ne bayan rasuwar Kalifa Sheikh Isyaka Rabiu Kano tun a shekarar 2018.
A cikin watan maris, an yi hasashen nadin tsohon Sarki Sanusi II a matsayin kalifan yayin gudanar da gagarumin maulidin Sheikh Ibrahim Inyass na bana da ya gudana a Sakkwato. Sai dai daga bisani an samu sanarwar cewa nadin bai tabbata ba, farfaganda ce kawai.
Sanarwar da ta fito daga wani mai magana da yawun Sheikh Mahi ta bayyana cewa,
“Muna sanar da kowa, kuma duk mai kira ya yi kira cewa ma’abocin kullawa da warwarewa da zartarwa a cikin sha’anin Faidhar Tijjaniyya, wanda shi ne Khalifa Sheikh Mahi Inyass (RTA) ya nada tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi Halifan Tijjaniyya a Nijeriya.

“A bisa wannan zartarwar, muna rokon Ubangiji cikin kankar da kai da ya karfafe shi bisa daukan wannan nauyin da aka dora masa, kuma ya aiwatar da ita kamar yadda aka yi tsammani ko fiye da haka. Muna rokon Allah madaukakin Sarki da ya datar da shi zuwa ga sauke nauyin da ke kansa kuma ya sanya hakan ya zama mai amfani ga dan Adam, Amin” In ji Abubakar Sirrin Baye Inyass.

Sanarwar ta ce an yi nadin ne a ranar Lahadi da dare bayan addu’ar khatamar Alkur’ani da ya gabata a Kaulaha inda tsohon Sarki Muhammadu Sunusi II ya samu halarta.

Sai dai kuma, a martanin da ya mayar sport da nadin sabon kalifan, Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce irin wannan nadin na kalifanci ba su san da shi ba a darikar Tijjaniyya.

“Zuwan Khalifa Mahiy Inyass Nijeriya (a wata Maris) an rriga da an tattauna an daddale a gabanshi cewa babu wani abu mai kama da haka a Tijjaniya. A iya sani na Gausi ne kawai yake nada Khalifa a Faidha ba wani nad’adde ba. Sannan wanda aka nada ba cikakken dan Faidha ba ne, sojan gonan Wahabiyawa ne, domin har yanzu bai daina karantar da Littattafan su ba  kamar Littafin Ibnul kayeem dalibin Ibn Taimiyya yana Kafurta Abi-Talib da su Ibnul Jauzy. Irin Wannan ya za a yi mu amshe shi a Khalifanmu”, kamar yadda Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar da safiyar Talatar nan.
Har ila yau, a yayin da bangaren Sheikh dahiru Usman Bauchi suka yi fatali da nadin sabon kalifan, shi kuwa Alhaji Ibrahim Shehu Mai Hula wanda aka fi sani da Shehi Shehi Mai Hula, dan Kwamitin Majalisar Shura ta darikar Tijjaniya, kuma har ila yau shugaban Kwamitin Musabakar Alkur’ani ta Jihar Kano ya bayyana farin cikinsu ne da nadin da aka yi wa tsohon Sarki Sanusi II.

Ya ce, “wannan tarihi ne ya maimaita kansa, domin Kakansa ma kafin barinsa duniya sai da aka yi masa Kalifancin darikar Tijjaniya, saboda haka mu a nan Kano muna dada godiya ga Allah, domin wannan bawan Allah idan gado ake ya gada, idan batun Ilimi ne ya cancanci hakan.”

Da aka tambaye shi shin ko an tuntubi duk wadanda ya kamata kafin hakan ta faru? Sai ya amsa da cewa “wannan ai daman haka tsarin yake tun zuwan da Shehi Mahi ya yi Kano, duk sai da ya tuntube mu, haka ko ina a duniya sai da aka sanar tare da tattauna tsarin kuma Alhamdulillah Allah ya tabbatar da hakan.”

Akarshe ya yi addu’ar fatan Allah ya bashi ikon gudanar da ingantaccen jagoranci.
Yanzu dai al’ummar Nijeriya ta zuba ido ta ga yadda lamarin zai kaya musamman a tsakanin wadanda suke son nadin sabon kalifan da kuma wadanda suke bara’a da lamarin, shin wane bangare ne zai hakura ya rungumi kaddara.

- Advertisement -