Rikicin Kabilar Waja Da Lunguda: Gombe Ta Tallafa Wa ‘Yan Gudun Hijira A Balanga  

0
120

Rikicin Kabilar Waja Da Lunguda: Gombe Ta Tallafa Wa ‘Yan Gudun Hijira A Balanga  

Daga Khalid Idris Doya, Gombe

A kokarinsa na ganin ya tausaya da agaza ma wadanda suka yi gudun hijira sakamakon rikicin da ya faru a tsakanin ‘yan kabilar Waja da Lunguda a karamar hukumar Balanga, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya amince da kai daukin kayan abinci domin rage wa ‘yan gudun hijirar radadin halin da suka tsinci kansu a ciki sakamakon wannan rikicin da ya tilasta musu barin muhallansu.

Shugaban kwamitin rabon wanda kuma shine kwamishinan tsaron cikin gida a jihar, Adamu Dishi Kupto, a lokacin da ya jagoranci kwamitinsa zuwa kai kayan agajin zuwa sansanin ‘yan gudun hijira a Balanga ta Kudu da ta Arewa, ya bayyana cewar gwamnan ya umarce su da su kawo kayan tallafin ne domin tausaya da nuna damuwa kan halin da suka tsinci kansu a ciki.

Da yake jawabi ga ‘yan gudun hijirar a sansaninsu da ke Dala-Waja, Bwagal, Futuki, Sikkam,Cham,Yolde da kuma Bambam, Alhaji Adamu Kupto, ya mika jajen gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya garesu bisa wannan halin da suke ciki, sai ya basu tabbacin gwamnati na samar musu da kariya na lafiya da rayukansu.

Daga nan sai ya bada tabbacin gwamnati na yin duk mai yiyuwa domin zakulowa da hukunta dukkanin masu hannu a wannan danyen aikin na jawo rikici a tsakanin al’umma.
Ya bukaci shugabanin da aka basu kayan don su rabar da su tabbatar da yin adalci ga kowa da kowa domin haka ya cimma ruwa.

Da suke amsar tallafin, jagororin sansanin ‘yan gudun hijirar da suka hada da Habu Salim, Micheal Bulus, Reverend Abraham Uche da Dimon Awa na Bwagal, Sikkam, Cham, sansanin Yolde bi da bi, solar nuna godiyarsu wa gwamnan bisa wannan tallafin da ya musu tare da bada tabbacin yin amfani da su ta hanyoyin da za s taimaka musu.

Idan za ku iya tunawa ma, tun bayan barkewar wannan rikicin gwamnatin jihar ta dauki matakin sanya dokar hana fita a yankunan da abun ya shafa domin ganin an shawo kan rikicin, lamarin da ya sanya gwamnan da kansa kai ziyara wuraren da abun ya shafa domin jajantawa da nemo bakin zaren matsalar.

What's On Your Mind?