Rikicin kabilanci ya sake ballewa a wani yankin jihar Gombe, an kona gidaje 50

0
122

Rikicin kabilanci ya sake ballewa a wani yankin jihar Gombe, an kona gidaje 50

A wani harin ‘yan bindiga, akalla gidaje 50 ne suka kone tare kayan gona a wani sabon rikicin kabilanci a garin Nyuwar, na Jessu da ke jihar Gombe, The Punch ta ruwaito.

Ku tuna cewa an kashe mutane 19 tare da daruruwan gidaje da ba a san ko su waye suka lalata ba a rikicin Waja/Lunguda.

Yan bindiga sun afka Rugar Fulani sun kashe 12, sun ƙona gidaje da dama

Wani shaidar gani da ido, Ily Maisanda, ya ce tuni mazauna garin suka tafi Yolde don tsare kansu, in da ‘yan bindigan suka yi amfani da wannan dama wajen kai sabon hari a Nyuwar ranar Lahadi.

Maisanda ya ce, “Mazauna garin na iya ganin wutar daga Yolde. Wasu daga cikinsu (maharan) an kama su a cikin Cham bayan solar kwashe hatsi daga gidajen da ba kowa.

“A halin yanzu, babu wani taimako da ke zuwa daga gwamnati; magana kawai suke yi, rikici ne mai zafi.”

Wani mazaunin, Musa James ya ce, “Dare ne da ba hutu saboda wasu sassan Nyuwar-Sakku Luko, da wasu gidaje na Lunguda solar sake konewa.

Hakanan, wani Dennis Kujir ya kara da cewa ‘yan bindigar solar afkawa kauyukan a ranar Asabar da safiyar Lahadi.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Ishola Babaita, ya tabbatar da harin, ya kara da cewa mutanen sa solar dakatar da karin barna.

A wani labarin, Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja ta kashe ‘yan bindiga shida a yayin wani samame na dakile harin da ‘yan ta’addan suka kai a yankin Garkogo, The Nation ta ruwaito.

An ce ‘yan bindigar solar kai hari a wasu kauyukan da ke kusa da Garkogo amma rundunar hadin gwiwar ta fatattake su.

Bayanai solar ce rundunar ta dauki matakin ne bayan wani labari da ta samu kan harin da aka kai kauyukan a safiyar ranar Asabar inda suka yi kwanto da ‘yan bindigan.

Supply: Legit.ng

What's On Your Mind?