Rigima Ta Kare: Gwamnati Da ‘Yan Kwadago Sun Hau Teburin Sulhu A Kaduna

- Advertisement -

Rigima Ta Kare: Gwamnati Da ‘Yan Kwadago Sun Hau Teburin Sulhu A Kaduna

Daga shehu Yahaya, Kaduna

Yadda Yajin Aikin Ya Shafi kanana Da Matsakaitan Masana’antu

Bisa ga dukkan alamu al’ummar Jihar Kaduna ta numfasa, sakamakon dakatar da yajin aikin da kungiyar kwadago ta NLC ta yi na kwana biyar domin hawa teburin sulhu da gwamnati don warware sabanin da ke tsakaninsu sport da korar ma’aikata a jihar.

‘Yan kwadagon solar amince da dakatar da yajin aikin ne na kwana biyar a yayin da ya shiga kwana na uku, bayan gwamnatin tarayya ta bukaci bangarorin da su zauna a kan teburin sulhu domin lalubo hanyar da za a warware matsalar.

A wani taron manema labarai na gaggawa da kungiyar kwadagon ta yi da yammacin jiya Laraba a Otel din Assa Pyramid da ke kaduna, ta ce ta dakatar da yajin aikin ne musamman domin sanya bakin gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa Kwamared Ayuba Waba, shi ne ya bayyana hakan inda ya ce yanzu za su hau kan teburin sulhu da Gwamnatin Jihar kaduna wanda za su fara a yau Alhamis a  Abuja domin ganin an cimma matsaya a kan bukatunsu.

Ayuba Waba, ya ce zuwa gobe za su sanar da matsayar da suka cimma a tsakaninsu da gwamnatin jihar Kadunan da ta tarayya.

Shugaban ya gode wa daukacin ma’aikata da sauran al’ummar jihar bisa hadin kai da goyon bayan da suk basu a yayin gudanar da yajin aiki a jihar.

Yajin aikin na kungiyar kwadago ya jefa jihar Kaduna cikin mawuyacin hali, lamarin da ya tagayyara al’ummar jihar baki daya.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin bangaren gwamnatin jihar amma ya ci tura inda ya tura wa kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomin jihar sakon kar ta kwana amma har ya zuwa lokacin da muke kammala rubuta rahoton babu amsa.

 

Daga Mustapha Abdullahi, Kaduna

…Tonon Sililin Wasu Mata Da Aka Yi Amfani Da Su Wajen kalubalantar ‘Yan kwadago

Wasu da suka ce an yaudare su ne zuwa wurin gangamin

Wadansu mata da aka kwaso domin su kalubalanci gangamin gangamin kungiyar kwadago ta kasa da take yi a Jihar Kaduna solar bayyana wa jami’an tsaro cewa yaudararsu aka yi da nufin za a yi taron siyasa ne, amma sai da aka kawo su kan marabar titin Golf course da hedikwatar ‘yan sanda ta kasa da ke Kaduna sai suka gane cewa ba gaskiya ba ne abin da ake gaya masu.

dimbin tarin matan solar tabbatar wa da gangamin ‘yan kungiyar kwadagon ne lokacin da suka tunkare su domin jin me yakawo su wajen taron a jiya Laraba.

Wadansu daga cikin ‘ya’yan kungiyar masu yin gangamin solar tambayesu cewa ku da kuke mata sanye da hijabi me kuka zo yi nan? Hakika kun ba mu kunya da muka ganku a haka”, inji yan kwadago.

Nan da nan sai wasu daga cikinsu suka ce an kwaso su ne da sunan wai za a yi taron siyasa, amma da suka zo wannan wuri sai suka ga ba haka ba ne yaudararsu aka yi da cewa za a yi taro kuma su ba su ga hakan ba domin abin da suka tarar wani abu daban ne.

Suka ce, “mu ba za mu tunkari taron jama’a mai yawa  irin wannan ba da sunan gangamin goyon bayan wani ko wasu ba, don haka mun yi nadamar zuwa wannan wuri har ga Allah saboda yaudara mu aka yi.”

Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin dai daukacin matan solar sulale daga wurin taron inda kowace ta kama gabanta.

Kuma Kwamishinan rundunar yan Sanda ta kasa reshen Jihar kaduna ya samu zuwa Kofar ofishin yan kwadago na kasa reshen Jihar Kaduna inda ya tattauna da manema labarai.

Inda kwamishinan ‘yan Sandan ya shaida wa manema labarai cewa ya fito ne ya na zagayawa domin ya tabbatar da komai na tafiya ba tare da samun wata matsala ba.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin biyu na ‘ya’yan kungiyar kwadago da Gwamnati  da su guje wa yin abin da bai dace ba.

Wata mata da ke cikin hotunan da ta tattauna da manema labarai ta ce su na son a samar da ruwa, wuta da sauran abubuwan extra rayuwa ne shi ya sa suka fito, amma da yawa daga cikinsu ba a gaya masu gaskiya ba ko me ya sa aka dauki su daga gidajensu saboda an ce masu za a yi taron siyasa ne a filin wasa na Rancahs da ke cikin garin Kaduna.

 

Daga shehu Yahaya, Kaduna

…Sulhu Tsakanin Gwamnati da ‘Yan kwadago Shi Ne Mafita – Jakadan Hayin Banki

A yayin da kungiyar kwadago ke ci gaba da gudanar da yajin aiki, an bayyana cewa hawa teburin shawara shine mafita dangane da halin da Jihar Kaduna ta tsinci kanta yanzu a ciki na takaddama tsakanin Gwamnan Jihar Kaduna da kungiyar kwadago ta kasa lamarin da ya sabbaba shiga cikin yajin aikin da talakawa ke ji a jikin su.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna mai suna Alhaji Abdullahi Gambo Abba lokacin da yake tsokaci dangane da yajin aikin da ke gudana yanzu haka a Jihar ta Kaduna.
Gambo Abba wanda ke rike da sarautar Jakadan Hayin Banki Kaduna ya ci gaba da cewar, zama teburin shawara tsakanin bangarorin biyu na da matukar fa’ida domin shi zai taimaka wajen lalubo bakin zaren da magance matsalar ba tare da cutar da sauran jama’a ba.
“Domin a halin da ake ciki yanzu babu masu shan wahala dalilin wannan yajin aikin sai jama’ar Jihar, wadanda yajin aikin ya jefasu cikin matsananciyar damuwa.
Daga karshe dan siyasar ya yi addu’a gami da fatan Allah daidaita tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin Jihar, domin abubuwa su dawo bisa ga tsari.

Yadda Yajin Aikin Kaduna Ya Shafi Masu kanana Da Matsakaitan Masana’antu

Daga Idris Aliyu Daudawa
Masu kanana da kum amatsakaitan masana’antu a Jihar Kaduna solar yi kira da gwkamnatin Jihar ta kawo karshen shi yajin aikin da ake yi, wanda kungiyoyin kwadago suka kira da ayi shi, domin hakan yana kawo masu cikas wajen harkokin tafiyar da kamfanonin nasu.
Manema labarai solar bada rahoton cewar ranar Litinnin ce kungiyar kwadago ta Jihar ta fara yin wani nyajin aiki na kwanaki biyar, wanda kuma   amatsayin na jan kunne ne, sabodsa a tilasta wa gwamnati kan matakin knowledge dauka na ma’aikatan da suka kora.
Wani mai yi walda, a Narayi mai suna, Ruphus Eke ya bayyana cewa shi yajin aikin ba karamin koma baya ya kawo ma harkar ta shi ba, wannan kuwa ya ksance ne a sanadiyar rashin wutar lantarki, domin idan ya ce zai yi amfani da injin janareto, daga karshe ba zai iya gane wa shi al’amarin ba.
Ya ci gaba da bayanin cewa “ Duk da yake fara shi yajin aikin ba wani abinda ba a so bane, sai dai kuma abubuwan da zai haifar daga karshe kuma ba masu dadi bane.
“Yanzu na ma rasa ko wanne hali nake ciki domin idan babu wutar lantarki ni kuma abin ban ma san yadda zan ce ba, ni duk na ta’allaka ne kan shi kamfanin na wutar lantarki. Kamar dai yadda ya bayyana”.

Ita kuma Irene Musa wadda take yin sana’ar kizo ne akan hanyar gidan waya, ta bayyanawa manema labarai cewa, ita yanzu ba zata fara wata maganar ribar da zata samu ba, domin kuwa tana kara amfani da kudin tane wajen sayen fetur da zata sawa Janareto.
Ta ci gaba da bayanin cewa “ Ni ba zan iya jurewa sayen fetur a kowacce rana ba, saboda kuwa su abokan harkar tawa sunfi son wurin da ayke da wutar lantarki.
“Ina fatan gwamnati za ta amince ta zauna da su shugabannin kungiyoyin kwadagon, idan aka yi hakan harkokin namu za su fi tafiya.
Ita kuma Esther Jacob, wadda ita ma tana tafiyar da ahjrkart kasuwanci a Jami’ar Jihar Kaduna ta ce, ba zata iya ci gaba da harkokin taba, saboda an rufe jami’ar.
Ta cigaba da karin haske inda kuma ta ce “Ba za ku iya sanin abin da yake faruwa  damu ba, domin yawancin mu mun  dogara ne akan kananan sana’aoi, domin mu biya bukataun kanmu da kuma ta ‘ya’yanmu.“
“Ina kira da dukkan wadanda abin ya shafa su kasance solar zauna a teburin yin sulhu, saboda hakan ne kawai zai sa mutane su ci gaba da harkokin da suka saba na samun kudaden da suke tafiyar da rayuwarsu.”

…Yadda Wasu Fusatattun Matasa Suka Farmaki Ofishin ‘Yan kwadago A Kaduna

Daga Shehu Yahaya, Kaduna

A dai-dai lokacin da yajin aikin da kungiyar kwadago takeyi a Kaduna ya shiga  kwana na uku, Wasu fusatattun matasa solar kai hari a ofishin kungiyar kwadago ta kasa NLC reshen jihar domin hana kungiyar ci gaba da yajin aikin da Takeyi a jihar.

Wakilinmu ya hango matasa sama da guda 100 dauke da makami da kwalaye suna fadin bamaso; bamayi, lamarin da ya haifar da dar-dar a zukatan mazauna jihar.

Matasan sunce basa goyon bayan yajin aikin da kungiyar kwadago take a jihar, inda suka ce suna tare da gwamnatin jihar na korar ma’aikata a jihar.

Wannan yunkurin hana yajin aikin da matasan suka yi a yau ,ya Sanya ‘yan kasuwa masu shaguna duk solar rufe shagunansu .

Wakilinmu ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandar jihar kaduna  ASP Mohammed Jalinge, inda ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa ba matasa zauna gari banza bane kadai suka gudanar da tarzomar ba harda mutanan gari.

Jalinge,yace  solar kama wasu daga cikin matasan da suka yadda rikicin wanda zasu ci gaba da gudanar da binciken.
Wakilinmu ya Nemi jin ta bakin shugaban kungiyar kwadago ta jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman,  yace basuyi mamakin hakan ba, inda yace tun farko fara yajin aikin matasa ‘yan ta’adda suka fara yunkurin tada rikici domin hana yajin aikin.

Ayuba Magaji Suleiman, ya ja hankalin jami’an tsaro da kada gwamnatin jihar kaduna tayi amfani dasu wajen cin zafarin jama’a, yana mai cewa suna gudanar da yajin aikin ne domin tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana mutunta rayuwar ma’aikata.

 

- Advertisement -