Rigakafin Korona: Facebook Ta kaddamar Da Gangamin Fadakar Da Al’ummar Nijeriya

0
69

Rigakafin Korona: Facebook Ta kaddamar Da Gangamin Fadakar Da Al’ummar Nijeriya

Daga Bello Hamza, Abuja

Hukumar Facebook ta bayyana kaddamar da wani manhaja a kafar sadarwata wanda mutum zai iya makalawa a kan hotonsa inda zai nuna cewa, mutum ya yi allurar rigakafin cutar korona ko kuma yana shirin yi a anan gaba shi da iyalansa.
Shugabar kamfanin a yankin Afrika ta Yamma, Adaora Ikenze, ta sanar da haka a ranar Juma’a a takarar manema labarai da aka raba.
Ta ce, Facebook za ta yi amfani da girma da kuma mutanen da take hulda dasu wajen isa ga dimbin al’umma a cikin kankanin lokaci, ta haka an taimaka wa mutane wajen fadakar das u bukatar yin allurar rigakafin cutar korona.
Ta kuma kara da cewa, sabon tsarin da Facebook ta fito da shi zai taimaka wajen yadda al’umma za su bayyana yadda aka yi musu allurar da kuma ta haka za su jawo hankalin abokai da iyalansu suma su gaggauta yin allurar, tunda an lura cewa, allurar rigakafin ya bazu a fadin Nijeriya baga daya a halin yanzu.
A jawabinsa, Dr Faisal Shuaib, shugaban hukumar ‘Nationwide Main Well being Care Debelopment Company (NPHCDA)’ ya nuna jindadinsa akan hadin kai a tsakanin sa da hukumar Facebook.
“Wannan hadin kai nada matukar mahimmanci za kuma mu yi kokarin tabbatar da ganin an samu nasarar yadda ya kamata.
“Wannan hadaka zai taimaka wajen ganin al’umma da dama solar yi allurar rigakafin a fadin Nijeriya, “, inji Dr Shuaib.

What's On Your Mind?