Real Madrid Da Chelsea: Sai Anje London Za’a Bambance Aya Da Tsakuwa

0
80

Real Madrid Da Chelsea: Sai Anje London Za’a Bambance Aya Da Tsakuwa

Kungiyoyin Real Madrid da Chelsea solar tashi wasa 1-1 a karawar farko ta dab da kusa da karshe a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League da suka kara ranar Talata a Spaniya.

Minti hudu da fara wasan Chelsea ta ci kwallo ta hannun dan wasanta na gaba, Christian Pulisic, sai dai Real Madrid ta farke ta hannun dan wasanta na gaba, Karim Benzema tun kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Dan wasa Pulisic ya zama dan kasar Amurka na farko da ya ci kwallo a gasar cin kofin na zakarun turai na Champions League a dab da karshe, shi ne kuma matashin dan wasan Chelsea da ya zura kwallo a raga a gasar, mai  shekara 22 da kwana 221 a duniya.

Shi kuwa dan wasa Karim Benzema, ya ci kwallo ta 71 a Champions League jumulla, hakan ya sa ya zama na hudu a jerin wadanda suka yi wannan bajintar tare da tsohon dan wasan kungiyar, Raul Gonzalez.

Wadanda ke gabansu solar hada da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Cristiano Ronaldo da kyaftin din Barcelona, Lionel Messi da kuma dan wasan gaban Bayern Munchen, Robert Lewandowski.

Ranar Laraba 5 ga watan Mayu kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kai ziyara filin wasa na Stamford Bridge dake babban birnin London domin buga wasa na biyu a Champions League.

Real Madrid ta lashe Champions League 13, Chelsea kuwa sau daya ta taba dauka shi ne a kakar 2011/12.

Bugu da kari, wannan shi ne karo na 30 da Real Madrid ta buga a wasan dab da karshe a Zakarun Turai, ita kuwa Chelsea ta yi na takwas ne sannan Real Madrid ta lashe guda 13 yayin da Chelsea take da guda daya.

‘Yan wasan da suka buga wa Real Madrid wasan :

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da E. Militao da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Isco da Arribas da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.

Tarihin Haduwar Kungiyoyin Biyu

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ziyarci abokiyar hamayyarta wato Real Madrid domin buga wasan farko na dab da karshe a gasar zakaru ta Champions League da suka fafata ranar Talata a Spaniya.

Real Madrid ta kara da kungiyar Chelsea karo uku ba ta taba samun nasara a kan kungiyar ta Stamford Bridge ba, ita ce wadda Real Madrid ta kasa ci a gasar zakarun Turai har kawo wannan lokaci.

Kungiyoyin biyu solar fafata a shekarar 1971 a gasar cin kofin Cup Winners Cup inda suka tashi 1-1 a wasan farko a na biyu kuwa Chelsea ta yi nasara da ci 2-1 sannan solar hadu a shekarar 1998 inda Chelsea ta doke Real Madrid ta kuma lashe Uefa Tremendous Cup da ci 1-Zero.

Wannan shi ne wasa na 163 a Uefa Champions League tsakanin kungiyar Ingila da ta Spaniya, inda a wasa bakwai ba ya kungiyoyin Ingila solar yi nasara a hudu da canjaras biyu da rashin nasara daya.

Wannan shi ne karo na takwas da Chelsea za ta buga karawar dab da karshe a Champions League, ita kuwa Real Madrid za ta fafata ne karo na 14 wanda hakan ya sa ake ganin kowacce kungiya tana da dama.

Wasa daya Chelsea ta yi rashin nasara a fafatawa bakwai a wasan farko na dab da karshe a Champions League, inda ta ci biyu da canjaras hudu, sai kungiyar Monaco da ta doke ta Three-1 a shekarar  2003 zuwa 2004.

Real Madrid ta ci wasan zagayen farko tara daga guda 10 a Champions League karawar zagaye na biyu da rashin nasara a wasa daya haka kuma wannan shi ne wasan farko da Real Madrid ta yi na dab da karshe tun shekarar 2017 zuwa 2018, inda ta yi nasara a wasan farko da ci 2-1 a gidan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich.

Mai koyar da ‘yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane da kuma na Chelsea, Thomas Tuchel suna daga cikin masu koyarwa 24 da suka ja ragamar wasa sama da 15 tun daga zagaye na biyu a Champions League.

Kocin na Chelsea, Thomas Tuchel ya fusaknci Real Madrid ba tare da rashin nasara ba a Champions League sau hudu, inda ya ci daya da canjaras uku kuma Zidane bai taba samun nasara a kansa ba.

A tarihin gasar cin kofin zakarun turai na Champions League, wani kocin da ya fuskanci Real Madrid sau hudu ba tare da ta yi nasara a kansa ba shi ne Gerard Houllier da ya yi nasara a biyu da canjaras biyu.

What's On Your Mind?