Rasuwar Sanata A’isha Alhassan Ba Karamin Rashi Bane Ga ‘Yan Nijeriya – Ministar Mata

- Advertisement -

Rasuwar Sanata A’isha Alhassan Ba Karamin Rashi Bane Ga ‘Yan Nijeriya – Ministar Mata

Daga Idris Aliyu Daudawa

 

 Ministan harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta bayyana cewar rasuwar Aisha Jummai Al-Hassan a matsayin wani babban rashi ne na al’ummar Nijeriya.

 

Tallen ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da take dauke da sa hannun  Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Mista Odutayo Oluseyi, ranar Asabar a Abuja.

 

Ministar ta bayyana ta nuna matukar kaduwa wajen jin labarin  mutuwar tsohuwar Ministar harkokin mata a kasar Masar, wanda aka fi sani da suna ‘Mama Taraba’.

 

“Mutuwar Aisha Jummai Al-Hassan ta kara da cewa wani babban rashi ne ga kasa da kuma duniyar mata musamman”.

 

Ministar ta bayyana wadda ta gada, a matsayin “wata kwararriyar ma’aikaciya, ‘yar siyasa mai kishin kasa, wacce a matsayinta na ministar harkokin mata, ta ba da gudummawa matuka wajen’ ‘yantar da mata da kuma ci gabansu a Nijeriya.”

 

Ta yi kira da iyalan da su ci gaba da yin hakuri cikin halin da suka samu kansu yanzu, da kuma addu’ar Allah ya jikanta ya kum rahamsheta.

 

Manema l;abarai solar bayyana cewar marigayiyar Al-Hassan, ta mutu tana da shekara 61 a duniya, Shugaban kasa Muhammadu Buhari shi ne ya nada ta a matsayin Ministar harkokin mata a shekarar 2015.

 

Amma, ta yi murabus daga matsayinta a watan Yuli na shekarar 2018 don tsayawa takara gwamna a zaben gwamna na 2019 a karkashin tutar jam’iyyar United Democratic Occasion (UDP).

 

Amma, ta sha kaye ne a hannun gwamnan Jihar mai ci yanzu, Darius Ishaku, wanda ya sake tsayawa takara a karo na biyu a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Occasion (PDP).

 

Kafin a nada ta Minista, Al-Hassan ta na da mukamin Sanata a karkashin jam’iyyar PDP mai wakiltar  mazabar Taraba ta Arewa.

- Advertisement -