Rasuwar Mama Taraba Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –Farfesa Gwarzo

- Advertisement -

Rasuwar Mama Taraba Babban Rashi Ne Ga Nijeriya –Farfesa Gwarzo

Shugaban rukunin Jami’o’in Maryam Abacha American College (MAAUN) da

Franco-British Worldwide College dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana haka ne daga kasar Farance A yau Litinin 10-5-2021 cikin wata takardan sakon taaziyyarsa ga yan uwa da dangin tsohuwar ministan wanda

Wanda Allah (SWA) yayi mata rasuwa ranar Asabar a kasar Misira

Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya ce ya san Marigayi jummai Alhasan a matsayin jajirtaciyar mace mai kamar maza kuma yar kishin Nigeria wacce zaa dade ana tunawa da ita

Shugaban na jamiar maryam Abacha American College Adamu Gwarzo, ya ci Gaba da cewa yan Nigeriya za su cigaba da tunawa da tsohuwar ministan a matsayin jaruman mace yar kishin kasa Nigeria

“A don hakan, ina mika sakon ta’aziyyata ga iyalai da ‘yan uwan marigayiya Hajiya Asha jummai da jamaar jihar Taraba tare da Daukacin Al ummar Nijeriya baki daya Allah ya kolanta yayi mata Gafara ‘, inji shugaban Jami’ar MAAUN.

- Advertisement -