Rasuwar Mai Babban Daki Babban Rashi Ne Ga Nahiyar Afirka -Dansaran Kano

0
116

Rasuwar Mai Babban Daki Babban Rashi Ne Ga Nahiyar Afirka -Dansaran Kano

Daga Ibrahim Muhammad,

Dansaran Kano Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya bayyana rasuwar mai babban daki mahaifiya ga Sarkin Kano  Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado da cewa babban rashi ne baga masarautar Kano da Ilori kadai ba rashi ne ga al’ummar jihar Kano da Arewacin kasarnan da nahiyar Afirka gaba daya.

Ya ce, mai babban daki matar marigayi mai martaba Alhaji Ado Bayero ce Allah ya jikansa da rahama wacce itama rasuwarta an yi  rashi na uwa ta gari wacce ta rungumi duk ya’ya a matsayin nata ba tare da nuna banbanci ba, suna fata Allah ya gafarta mata.

Ya ce, ita marigayiya Mai babban daki gaba da baya a cikin sarauta ta tasoyar sarki ce jikar sarki matar sarki kuma ‘ya’yanta sarakuna wannan ba karamar baiwa bace da Allah ya azurtata da shi yanta da danginta da wadanda suka zauna tare solar bayyyana kyawawan halayenta wanda abin koyi ne ga al’umma kuma wannan tasa mutane tawaga tawaga daga ciki da wajen kasarnan aketa tururuwa aka ta’aziyya da alhinin rashinta.

Alhaji Gambo Danpass ya yi kira ga al’umma su dagewa addu’oi domin neman taimakon Ubamgiji daga halin da ake ciki na tabarbarewar harkar tsaro da kullum yake dada kamari. Sannnan ya nemi hukuma ta dauki matakai na sassauta kaifin talauci a tsakanin al’umma domin ba zai yiwu da talauci a zauna lafiya ba sai an sassauta an dakile talauci ta bude masana’antu da budawa yan kasuwa hanya ta bunkasa saye da sayarwarsu a ciki da wajen kasarnan sai a sami zaman lafiya.

Dansaran na Kano Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya ce, ma’aikatan Gwamnati da ‘yan fansho a rika basu hakkokinsu sannan a kula da cigaba da bunkasa rayuwar matasa ta samar musu da sana’oi irin wadannan matakai zasu taimaka wajen inganta samarda zaman lafiya a tsakanin al’umma.

What's On Your Mind?