Rashin Wutar Lantarki Yana Karya Sana’armu – Alhaji Basiru 

0
66

Rashin Wutar Lantarki Yana Karya Sana’armu – Alhaji Basiru 

Daga Sani Tahir,

 

Alhaji Basiru Adamu yana daya daga cikin masu sana’ar man dafa abinci, matashin dan kasuwa kuma Shugaban Kamfanin. Basiru Adamu Basic Enterprises, ya yi kira da gwamnati ta kawo masu taimako cikin sana’arta su, saboda irin amfanin da take da shi a cikin al’umma. A zantawar da ya yi da Sani Tahir, ya yi bayanai daban- daban har ma da wadanda ba su a cikin maudu’in kamar haka:

 

Ko za ka bayyanawa masu karatu takaitaccen tarihinka?

 

Assalamu alaikum, ni dai Sunana Basiru Adamu,an haifeni a wani Gari da ake kira falsa wanda yake a karamar hukumar Tsanyawa ta Jihar Kano, acan ne  na fara karatun Firamare(major a wani Gari da ake ira da suna Dorayi,daga baya kuma na dawo unguwar Dakata da zama Inda nayi makarantar Allo da Sakandire(secondary)a Dakata.Daga  baya kuma muka fara harkokin kasuwancin tare da wani mai gidan mu Alhaji Ibrahim a nan muka samu gogewa har zuwa yanzu,daidai gwargwado har Allah ya kawo mu wannan halin da muke ciki.

 

A wacce shekara ka fara wannan sana’ar ta sayar da mai?

 

Mun tsunduma wannan sana’ar ta sayar da mai a shekarar (2003) a wani shago da ake kira na maliya, wasu ne a wurin tun farko,mu kuma, sai muka karbi wurin daga baya muka ci gaba da kasuwanci, anan unguwar Dakata a Bus Cease,na maliya,ke nan muna nan, inda har Allah yasa aka yanka Dakata A bangaren Masana’antu sai muka koma chan inda har yanzu munanan.Wanda a halin yanzu muna cikin sana’ar sosai da sosai Alhamdulillah.

 

Ko da ganin wannan aikin na ku ba zai yi yu a tsakanin mutum biyu ko uku ba me zaka ce kan samarwa matasa aikin yi a wannan kamfanin naka?

 

Masha Allah babu abinda zamu ce da Allah sai dai godiya ka san duk inda,aka ce kamfani duk da ba za’a iya kiran kanmu da kamfani restricted ba,to amma kamfani baya tafiya akan na mutum daya, yana tafiya akan jagorori ne, masu yawa ,ni ne Shugaban wannan kamfanin amma hakikanin gaskiya wadanda suke gudanar da kamfanin solar fini,jajircewa irin su Yakubu,Yusuf da sauransu, Wanda kamar su Manajiman ne,banda sauran leburori wadanda muna da su sama da mutum (80),da sune muke wannan aikace-aikacen.idan aka nika gyada,idan gyadar ta wuce sai mu koma kan angurya idan ita ma ta wuce, sai mu koma,kan waken suya,haka shima waken suyan da zarar ya wuce sa a tafi manja,da farin mai wanda ake kawo mana daga Kudu.wannan dai shi ne dan takaitaccen tarihin kamfani.

 

Gwamnatin tarayya tafi bada fifiko ga masu sana’ar manja,wanda alkaluma solar nuna cewar ana amfani da wannan man naku a nan gida, Nijeriya da kuma kasashen waje me zaka ce dangane da hakan?

 

A gaskiya muna kira da gwamnati kamar yanda take bawa ‘yan manja, mune muka fi cancantar da a tallafawa,domin mune muke nika gyada,wanda gyadar nan sau da yawai mun fi samota daga kasashen Chadi,Kamaru,da dai sauransu,to muna neman tallafinta da ta shigo yadda su wadancan ta,tallafa masu,muma knowledge tallafa mana a cikin al’amuranmu. Saboda abu ne wanda yake samarwa sama,da mutum tamanin (80) sune suke aiki a wannan gidan namu gaba daya.

To kaga muna bukatar gwamnati ta shigo cikin wannan sana’ar tamu domin idan ta shigo hakikanin gaskiya sama da mutum dubu za su samu aiki,a iya wannan kamfanin,bi’izinihi ta’ala,muna tunanin hakan tunda yanzu muna tafiya a dan karamin kamfanin, wanda idan ka samu tallafi abubuwan da zaka fadada ba karamin aiki ba ne.

 

Don Allah Gwamnati da ta dube mu,ta duba taga abinda zata iya yi mana,tai mana a cikin wannan tafiyar ko da tallafin manjan ne, tai mana ai muma muna manjan,wanda mu manjan sayowa muke daga wurinsu,Wanda inda zata bamu gudunmuwa muma zamu iya samar da manjan, muna da injinan da za su yi, mana da matatar da zamu mayar da manjan zuwa irin Olin, dan oda da ake shigowa dashi,daga waje,to da zamu samu tallafi duk zamu iya irin wadannan kayayyaki,matsalar dai  it ace karancin jari ne damu, shi yasa dole sai hakuri muke da wasu abubuwan, hakura muke dasu in sha Allahu.

 

Ko kuna da kungiya kuwa?

 

kwarai kuwa da akwai kungiyar mu mai suna (Dasoma),wanda Shugabanta na Jiha shi ne Sagagi,to akwai namu na nan shugabanta shi ne Musa sakatare, shi  mutumin Dawanau ne,

 

Wacce irin matsala kuke fuskanta ne?

 

Matsaloli ba za’a ce babu su ba,akwai su wadanda kuma suke da yawa,tun daga kan wutar lantarki, saboda kasan dizel ba zai yi  shi wannan aikin ba,da wutarb lantarki muke yi, sannan kuma babu isasshiyar wutar.Idan har an saki wutar nan ma muna,fuskantar biyan kudin ,muna jin labarin yadda su Legas, Enugu, Ibadan, suke biyan kudin wutar su,baya wuce kashi ashirin da biyar ba(25)amma mu kuma muna biyan kudin da ya kai sama da kashi hamsin da wani abu(50),Wanda mu anan gidan in har mun yi aiki a wata,muna biyan kudin wuta kusan Naira miliyan uku,wanda ba mu kadai ba. Akwai abokan mu wdanda suke Gombe, zaka ga abinda suke biya bai kai dubu dari biyu ba.

To gaskiya matsalar da muke fuskanta bata wuce uutar lantarki ba,tana durkusar da kasuwancin mu,saboda mu wadanda muke wannan sana’ar bamu da yawa, sauran solar durkushe,sai addu’a kawai.To kaga da gwamnati zata shigo maganar wutar lantarki ma kadai, banda tallafi,wallahi da gwamnati tayi mamakin yadda mutane za su samu aikace-aikace a nan gidan ma kawai, bama fadin kasuwar ba tunda yanzu ta zama kasuwar Jihar Kano,gaba daya, akwai masu yin Roba,da masu yin Fayib, Leda da dai sauransu,Wanda  da ace za’a samu  sassaucin kudin wutar lantarki da sai anyi mamakin mu nan gaba..

 

Menene sakonka na karshe?

 

Kira  na anan shi ne ina kira ga mutanen mu,dasu fito su jajirce,Hausawa suna cewa in kaji wane ba banza ba,ita gwamnati abinda  take bukata shi ne bibiya dole ba zamu zauna ba muce ko mai yazo ya similar mu ba, na daya  dai dole sai an jajirce ,muna da wakilai mutum zai kai kokensa,shi kuma wakili zai kai wurin da ya dace da wannan kuka, ya je duk da cewar muma muna da irin namu matsalolin, na mabiyan,da mutum ya fara bibiya   sau daya,biyu sai mutum ya nuna ya gaji, wani lokacin abu bai kai ya kawo ba,sai mu nuna gazawar mu, tofa daga lokacin da mutum ya nuna gazawar sai yayi wa kansa, saboda nuna gazawarka daga nan, kai da kanka ka fara bawa kanka matsala. Gazawarka daya sai ran da kaji ka a cikin kabari, abinda kayi ka gama wanda kuma baka yiba shikenan,

Kaga ma ai matukar kana raye wannan rayuwar sai ka jajirce,muna ganin wadanda bamu ba,yanda suke bibiyar abubuwa, wanda har sai solar samu nasara,mu kuwa da mun fara sai nuna gazawa ,ba zamu iyaba ,dole sai mutum ya fito ya jajirce sannan gwamnati ta san damu har da shugabannin mu, gaba daya.wannan shi ne sakona na karshe muna godiya

Ta nima ina godiya kwarai da gaske.

What's On Your Mind?