Rashin Tsaro: El-rufa’i Ya Nemi Tallafin Kudade Don Yakar Ta’addanci

0
105

Rashin Tsaro: El-rufa’i Ya Nemi Tallafin Kudade Don Yakar Ta’addanci

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya nuna damuwar sa dangane da karuwar satar mutane da fashi da makami a jihar da sauran sassan kasar nan.

Gwamnan ya ce lamarin na karuwa a kullum kuma lamarin yana da matukar ban tsoro, don haka yake neman tallafin kudade don kara kaimin hukumomin tsaro.

Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin gabatar da rahoton rubu’in farko na wannan shekara na Tsaro da Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta jihar ta gabatar.

Ya bayyana halin da ‘yan kasa ke ciki a yanzu haka a jihar ta Kaduna da ma kasa baki daya a matsayin abin takaici tayarda jama’a ke yanke tsammani da jami’an tsaron saboda yawan hare-haren.

A cewarsa, ‘yan ta’addan da ke gudanar da ayyukansu a cikin jihar ta Kaduna suna kara kusantowa daga kauyukan karkara zuwa biranen, inda suke kai hare-hare tare da kashe ‘yan kasa ba tare da tsoro ko dar-dar ba.

What's On Your Mind?