Rashawa Ba Za Ta Bar Nijeriya Ta Ci Gaba Ba, Inji Ganduje

0
121

Rashawa Ba Za Ta Bar Nijeriya Ta Ci Gaba Ba, Inji Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa kasar Nijeriya ba zata cigaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibaye ta.

Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis yayin kaddamar da wani kwamiti mai mutum takwas dasu gudanar da dabarun yaki da rashawa a jihar.

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Usman Alhaji ya wakilce shi, ya kaddamar da kwamitin ne a da nufin rage cin hanci da kuma tabbatar da gudanar da al’amura a bayyane a fadin jihar.

What's On Your Mind?