Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida: RSF Ta Yi Allah Wadai Da Kashe Su Da Ake Yi

0
84

Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida:  RSF Ta Yi Allah Wadai Da Kashe Su Da Ake Yi

Daga Sulaiman Ibrahim

Yayin da yau ake bikin ranar ‘Yan Jaridu ta duniya, kungiyar dake kare hakkokin ‘Yan Jaridu ta ’Reporters With out Borders’ tayi Allah wadai da kisan gillar da aka yiwa wasu Yan Jaridun kasar Spain guda biyu dake aiki a Burkina Faso, abinda ke dada nuwa hadarin dake tattare da wannan aiki.

Rahotanni manhajar Rfi yace an kashe dan Jarida David Berian da mai dauka masa hoto Roberto Fraile ne lokacin da Yan bindiga suka kai hari kan tawagar motocin gwamnatin da suke yiwa rakiya akan hanyar zuwa Gandun Dajin Pama.

Christophe Deloire, Sakatare Janar na kungiyar RSF ya bayyana mutuwar wadannan Yan Jaridu guda biyu a matsayin babban hadari ga aikin Jarida.

‘Yan Jaridun RFI

Deloire yace tun daga shekarar 2013 da aka kashe Ghislaine Dupont da Claude Verlon, ma’aikatan RFI har yanzu ba’a samu cigaba ba kan yadda Yan Jaridu zasu gudanar da aikin su cikin kwanciyar hankali a Yankin Sahel, musamman kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar.
Rahotan da aka gabatar na Yancin Jarida ranar 20 ga watan Afrilu, ya nuna cewar nahiyar Afirka na cigaba da zama mafi hadari ga Yan Jaridu, abinda ya kawo adadin Yan Jaridun da aka kashe zuwa 33 tun daga shekarar 2016.

What's On Your Mind?