Ranar ‘Yan Jarida Ta Duniya: Kafafen Labarai Su Guji Daukar Wadanda Ba Kwararru Ba – Dkt Piman

0
47

Ranar ‘Yan Jarida Ta Duniya:  Kafafen Labarai Su Guji Daukar Wadanda Ba Kwararru Ba – Dkt Piman

Daga Abubakar Abba,

A yayin da a daukacin fadin duniya ake gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya ta bana a yau three ga watan Mayun 2021, an gargadi kwararru a kafafen  yada labarai da ke a kasar nan, da su guji daukar wadanda ba su da kware wa a cikin aikin.

 

Domin ta hakan ne kawai za a magance  wadanda suke yawo kwararo-kwararo da wayar tafi da gidanka suke gabatar da kansu a matsayin ‘yan jarida, wadanda alhali ba su da wata kwarewa, ilimi ko wani horo da suka samu kan aikin na jairida.

 

Wannamn gargadin ya fito ne daga bakin Mataimakin Darakta na Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Yaki da Dumamar Yanayi a duniya Dakta Piman Hoffman.

 

Dakta Piman Hoffman ya kuma yi kira ga kafafen yada labarai da ke a kasar nan su dai na daukar su aiki domin kare martaba da kuma aikin na jarida, musamman idan aka yi la’akari da yadda irinsu ke bata wa aikin suna da kuma janyo wa aikin koma baya yau da kullum.

 

Ya kuma yi kira ga kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ da Cibiyoyin kula da kafofin yada labarai kamar su NPC NBC da sauran hukumomi su dinga tabbatar da ana kare rayuwar ‘yan jarida da ke a kasar nan, musaman a lokacin da suke kan gudanar da ayyukansu.

 

Ya kuma zargi wasu kafafen yada labarai  bisa yin amfani da  marasa kwarewa a kan aikin domin neman sauki, inda suke kin daukar wadanda suka cancanta da suka samu shaidar aikin jarida daga jami’oin kasar nan.

 

Ya kuma yi kira ga kafafen yada da su dinga biyan kwararrun ma’aikatan su albashi mai tsoaka, musamman idan aka yi la’akari da irin hadduran da suke samun kansu a yayin gudanar da aikin su.

 

Dakta Piman Hoffman ya kuma yi kira ga ‘yan jaridar da su guji yada labaran kanzon kurege su kuma hada kai da matakan gwamnati uku na kasar nan domin wallafa labaran zaman lafiya da ci gaban kasar.

What's On Your Mind?