Ranar Ma’aikata: Kungiyar Kwadago Ta Nemi Gwamnati Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro

0
65

Ranar Ma’aikata:  Kungiyar Kwadago Ta Nemi Gwamnati Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro

An Bukaci Su Nisanci Shiga Yajin Aiki

Daga Bello Hamza,

A ranar Juma’a ne wasu shugabanin kwadago suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara kaimi wajen kula da jin dadin ma’aikata da kuma gagauata maganin matsalar tsaro a fadin tarayyar kasar nan.

Solar yi wannan kiran ne a tattauanawa da manema labarai a daidai lokacin da Nijeriya ke shiga sahun sauran kasashen duniya na yin bikin ranar ma’aikata ta duniya, wato ‘2021 Staff Day celebration’.

Taken wannan bikin na wannan shekarar shi ne “COBID-19 Pandemic, Social and Financial Challenges for Respectable work, Social Safety and Welfare of the Folks.’’

Mr Issa Aremu, mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta NLC, ya ce babbar aikin gwamnati ita ce samar da kyakyawar shugabanci da kuma tsaro ga al’ummar ta.

Haka kuma wani mai suna, Mr Rimamshung Shama, wanda ma’aikacin gwamnati ne, ya bukaci gwamnati  a dukkan matakai su tabbatar da aiwatar da tsarin mafi karancin albashi da aka amince da shi ga ma’aikata.

“Abin takaici ne tun da aka amince da tsarin mafi karancin albashin, har yanzu ya zama matsala a wasu jihohi, gwamnoni su ki aiwatar da shi, ’’inji shi.

Shama, ya kuma bukaci gwamnati ta samar da kyakyawan yanayin da ma’aikata za su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Haka kuma, Mr Godswill Anucha, ya nemi gwamnatin tarayya ta gaggauta yin maganin matsalar tsaro da ke fuskanta a fadin tarayyar kasar nan.

 

What's On Your Mind?