Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Nijeriya Ta Sanar Da Ranar Hutu

0
96

Ranar Ma’aikata: Gwamnatin Nijeriya Ta Sanar Da Ranar Hutu

Daga Sulaiman Ibrahim

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana Litinin, three ga Mayu, 2021 a matsayin ranar hutu don bikin ranar ma’aikata ta duniya ta bana.

Ministan cikin gida, Rauf Adesoji Aregbesola, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya a cikin wata sanarwa da Shuaib Belgore, Babban Sakatare na ma’aikatar ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Yayin da yake taya Ma’aikatan Nijeriya murnar ganin wannan biki na wannan shekarar, ya yaba musu bisa hakuri, fahimta da goyon baya da suka nuna wajen tafiyar da manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kokarinta na ciyar da kasar zuwa mataki na gaba don kara tattalin arzikin kasar.

Aregbesola ya yi kira da a kara himma da kishin kasa daga dukkan ma’aikatan Nijeriya da kungiyoyin kwadago, yana mai cewa kalubalen da ake fuskanta na wannan lokacin, ba da dadewa ba za a kawo karshen su kasancewar gwamnati ta himmatu wajen tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.

“Gwamnati na sanya dukkan dabaru don dakile kalubalen rashin tsaro da ya turnuke sassan kasar.

“Don haka, ina kira ga kungiyar kwadago da dukkan ‘yan kasa masu kishin kasa da su jajirce matuka wajen tabbatar da cewa kalubalen tsaro ya zo karshe kamar yadda ya kamata.” Ministan ya jaddada hakan.

What's On Your Mind?