Ranar Alhamis Shugabannin Rundunonin Sojoji Za Su Gana Da Majalisar Dattawa

- Advertisement -

Ranar Alhamis Shugabannin Rundunonin Sojoji Za Su Gana Da Majalisar Dattawa

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Ranar alhamis mai zuwa ce manyan hafsoshin sojojin Nijeriya za su yiwa majalisar dattawa bayani kan halin da tsaron kasar nan yake ciki.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan,  shi ne wanda ya bayyana hakan, a lokacin da aka fara zaman majalisar  ranar Talata ta wannan makon a Abuja.

Tun farko dai an tsara su bmanyan hafsoshin za su yi bayanin ne ranar Talata amma sai aka sauya, saboda sauya masu wuri saboda taron majalisar tysaro ta kasa.

Rahotannin solar nuna cewa majalisar ta yanke hukunci da kuma daukar mataki ne a ranar 27 ga Afrilu, cewar zata kira  su manyan hafsoshin domin su yi masu bayanai, akan wannan irin shiri ko kuma tsarin da suka yi,wajen daukar matakai dangane da tabarbarewar tsaron da ake fuskanta a kasa.

Shi dai kudurin na majalisa ya biyo bayan wata maganar oda da Sanata Sani Musa jam’iyyar APC daga Jihar Neja ya gabatar.

An gabatar da shi kudirin ne a kan ayyukan ‘yan bindiga da’ yan ta’addan Boko Haram a wasu kananan hukumomin Neja da wasu sauran sassan Nijeriya.

“A yau, majalisar tsaro ta kasa na ci gaba da taron da ta fara a makon da ya gabata. Saboda haka, shugabannin tsaron da aka gayyata ba za su iya samun damar zuwa nan su yi mana bayani ba.

“Ba mu kuma da tabbacin cewa ko za su gama taron nasu a yau (Talata). Muna tsammanin cewa watakila har zuwa gobe laraba za a ci gaba da yin shi taron.

“Don haka don abin ya kasance  a cikin tsanaki shi yasa, yanzu muka sa ranar da za a gabatar da jawabin, ta  ranar Alhamis, 6 ga Mayu 2021.

“Ina so in yi kira ga dukkanin mu cewar su bayanan  da su manyan hafsoshin na Nijeriya da sauran jami’an tsaro za su yi mana, ko shakka babu  za su taimaka mana wajen hasken da zamu fahimta ya kuma taimaka mana kwarai da gaske.

“Kuma idan akwai need bukata ta karin kasafin kudi,  zamu iya fahimta ko ganewa sosai,domin muna iya amincewa da irin wannan bukatar.

- Advertisement -