Ramadana: Matar Gwamnan Bauchi Ta Yi Rabon Tallafin Kayan Masarufi Ga Mata

0
97

Ramadana: Matar Gwamnan Bauchi Ta Yi Rabon Tallafin Kayan Masarufi Ga Mata

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Uwar gidan gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Aishatu Bala Muhammad ta rabar da kayan masarufi da na koyon sana’o’in dogaru da kai wa mata a fadin kananan hukumomi 20 da suke jihar domin agaza musu da taimaka wa rayuwarsu a cikin wannan watan mai alfarma.

Da take mika kyautar kayan ga shugabannin mata na kananan hukumomi 20 a gidan gwamnatin Bauchi, Hajiya Aishatu Bala, ta bayyana cewar tallafin an tsara yinsa duk watan Azumi ne domin rage wa matan halin kunshi na rayuwa tare da saukaka musu dawainiyar rayuwar yau da gobe.

Matar gwamnan ta hori shugabannin da aka damka wa alhakin rabon a kananan hukumomin jihar da su tabbatar da aiken ya shiga hannun wadanda aka bada tallafin domin su, tana mai cewa a kowani lokaci gwamnatinsu na mutunta al’ummomin karkara da na birane.

Aisha ta nemi wadanda suka ci gajiyar wannan kyautar nata da su maida hankali wajen yin amfani da ababen da suka samu ta hanyoyin da suka dace domin kyautata rayuwarsu a kowani lokaci, tana mai cewa ta hanyar ririta ababen sana’a da aka samar wa al’umma za a iya rage kaifin matsalar rashin aikin yi da ke addabar jama’a a fadin kasar nan.

Da take yaba wa mai dakin gwamnan, Shugabar mata na jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, Hajiya Hafsatu Adamu, ta jinjina wa matar gwamnan a bisa kokarinta na ganin ta share wa mata hawaye a kowani lokaci, ita ma, ta jawo hankalin shugabanin matan da aka damka wa kayan a hannunsu da su yi aikin rabon misa adalci da gaskiya.

Daga cikin kayan da matar gwamnan ta yi rabiyar har da injinan markade, kayan aminci da suka ahda da suga, masara, shinkafa, da sauran kayan extra rayuwa.

What's On Your Mind?