Ramadan: Sanata Uba Sani Ya Raba Tallafin Azumi

0
58

Ramadan: Sanata Uba Sani Ya Raba Tallafin Azumi

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

A yayin da Musulmai suka fara Azumin watan Ramadan mai albarka, Sanata mai wakiltar Al’ummar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Dakta Malam Uba Sani ya kaddamar da rabon kayan tallafin abincin Azumi ga Al’ummar kananan hukumomi bakwai dake daukacin mazabunsa. kananan hukumomin solar hada da; Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Kaduna ta Arewa, Kaduna ta kudu, Cikun da kuma karamar Hukumar Kajuru.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da aka fitar wacce ta sami sa hannun mai taimaka ma Sanata Uba Sani akan abin da ya shafi harkokin mazabunsa, Arch Abubakar Rabiu Abubakar, wanda kuma aka rabama manema labarai.  Inda sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, rabon kayan abincin Azumin wannan shekarar ya hada da; Buhunan Shinkafa, Gyero, Wake, Taliya, Macaroni da kuma Sukari.

A cewarsa, “Har-ila yau, ganin yadda aka fara Azumin Watan Ramadanan, wannan rabon kayan abincin Azumin ya hada da; kungiyoyin Addinai, kungiyoyi masu zaman kansu, kungiyoyin Mata da na Matasa, Cibiyoyin Gargajiya, kungiyoyin Marasa Galihu, kungiyoyin Matasa ‘Yan Yanar Gizo wanda a turance ake kira da (social media crew).”

Sauran solar hada da; Shugabannin Jam’iyyar APC na shiyya, (Zone 2), Fitattun masu zaben fidda gwani (edcos),  masu ruwa da tsaki, Amintattun Jam’iyyar APC daga kowane bangare na shiyya, Sarakuna da sauran Al’umma.

Arch Abubakar Rabiu Abubakar, ya kara da bayyana cewa, “Wannan ba shi ne karo na farko da Sanata Dakta Malam Uba Sani ke bayar da tallafinsa ga Al’umma ba, domin idan ba’a manta, ko a makonnin da suka wuce, sai da Sanata Uba Sani ya kai irin wadannan Kayan tallafin abinci da makuden kudade zuwa wurare daban daban na ‘yan gudun hijira wanda ibtala’in ‘Yan Bindiga da masu garkuwa da Mutane ya rutsa da su.”

“Ina mai tabbatar maku da cewa, a kullum burin Sanata Uba Sani bai wuce na ganin ya kawo ma Al’ummarsa da abubuwan ci gaba ba, wannan dalilin ne ya sanya Sanata Uba Sani ya bayar da umurnin a Gina Bohol irin na zamani a kowane Unguwa dake Yankin mazabunsa, sannan ya bayar da umurnin sanya Sola mai dauke da hasken Rana a kowane wajajen ibadu domin saukakawa Al’umma ta yadda zasu bautawa Ubangijinsu cikin jin dadi da walwala.” A cewarsa.

What's On Your Mind?