Ramadan: Gwamnatin Borno Ta Raba Wa Magidanta 34,000 Abinci 

0
116

Ramadan: Gwamnatin Borno Ta Raba Wa Magidanta 34,000 Abinci 

Daga Muhammad Maitela,

Mukaddaahin Gwamnan jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, ya kaddamar da raba kayan abinci, tallafin Azumin Ramadan ga magidanta 34,000 Maiduguri.

 

Kowane magidanci ya samu tallafin buhun shinkafa, masara, gero, wake masu nauyin 25kg, tare da katon na taliya da sauran su.

 

Da yake jagorantar kaddamar da raba kayan abincin, a birnin Maiduguri a ranar Asabar, Hon. Kadafur ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakin tallafa wa jama’ar domin rage musu wahalhalun matsin rayuwar da ake ciki a wannan wata na Ramadan.

 

Ya kara da shaidar da cewa wadannan kayan abincin tallafi ne wanda Alhaji Aliko Dangote, A. A Rano hadi da kungiyar jinkai ta Baba For All, a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari da makamantan su.

 

“Har wala yau, gwamnatin jihar Borno ta bukaci daidaiku da kungiyoyi su yi koyi da irin wannan hubbasar da masu bayar da tallafin suka yi.” In ji Kadafur.

 

Bugu da kari kuma, Hon. Kadafur shi ne ya wakilci Gwamna Babagana Umara

Zulum wanda ya tafi aikin Umara a Saudi Arabia, ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin kayan abincin da cewa su yi amfani dasu bisa ga yadda aka tsara.

 

Har wala yau ya bukaci suyi amfani da lokacin wata Ramadan mai alfarma wajen addu’ar neman samun dawamamen zaman lafiya a jihar Borno da kasa baki daya.

 

Daga bisani, shugaban kwamitin raba kayan tallafi a jihar Borno kana kuma kwamishina a ma’aikatar ayyukan noma, Engr. Bukar Talba, ya yi karin haske da cewa wadanda suka ci gajiyar tallafin solar fito daga kwaryar birnin Maiduguri (MMC) da Jere, tare da bayyana cewa za a raba tallafin a sauran baki dayan kananan hukumomin jihar 27- an had been wa kowace gunduma mutum 1500.

What's On Your Mind?