Ramadan: Dan Majalisa Ya Tallafa Wa Mazabarsa Da Kayan Abinci A Borno

0
104

Ramadan: Dan Majalisa Ya Tallafa Wa Mazabarsa Da Kayan Abinci A Borno

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

dan Majalisa mai wakiktar Jere a majalisar wakilai ta tarraya, Hon. Ahmed Satomi, ya yi wa jama’ar mazabarsa goma ta arziki, musamman masu karamin karfi, da tallafin naira miliyan 47 tare da kayan abinci a watan azumin Ramadan a jihar Borno.

A cikin wannan adadi na naira miliyan 47, dan majalisar ya raba wa mutum 250 tallafin naira miliyan 25 wanda kowane mutum daya ya samu naira 100,000.

Kana saura naira miliyan 22 aka yi amfani dasu wajen sayo buhunan shinkafa, sikari da kayan masarufi domin raba wa jama’a.
Da yake kaddamar da tallafin a Maiduguri, Engr Satomi ya bayyana cewa, wannan wani bangare ne a kokarinsa wajen ganin ya ci gaba da kyautata wa al’ummarsa, inda ya ce tallafin zai ci gaba a shirin taimaka wa matsakaita da kananan yan kasuwa don bunkasa kasuwancin su a makonni masu zuwa.
Hon. Satomi ya kara da cewa, baya ga wannan ya dauki nauyin karatun daruruwan matasa a mazabarsa a matakin sakandire da makarantun gaba da sakandire, tare da bayyana cewa ya gina ajujuwa a karatun da dama a yankin da yake wakilta a karamar sakandiren Zabarmari/ Khadamari da sauran su a yankin.

“Saboda haka zan yi amfani da wannan dama na mika godiyata ga baki dayan al’ummar mazabar Jere dangane da cikakken goyon baya da hadin kan da suke bani, wanda ina matukar alfahari da girmama ni da kuka yi a matsayin na wakikceku a zauren majalisar wakilai ta tarayya.”

“Har wala yau, wannan tallafi ne da nake raba wa a kowace shekara, wanda na kuduri aniyar aiwatar dashi domin rage wa jama’armu halin da ake ciki na tsananin rayuwa a watan Ramadan.”
A nashi bangaren, a madadin jama’ar da suka ci gajiyar tallafin, shugaban karamar hukumar Jere, Hon. Umar Gujja Tom tare da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, Alhaji kachalla Mai Fata, solar yaba da kokarin dan majalisar dangane da wannan tallafi a lokaci irin wanna tare da shan alwashin gudanar da raba kayan bisa gaskiya da adalci ga wadanda suka cancanta.

What's On Your Mind?