Radi: Budurwa Ƴar Arewa Ta Roƙi Mahaifin Ta Yayi Mata Aure, Ko Na Dole Ne

0
544


Wata matashiya yar arewa ta gaji da zaman kadaici don haka ta je shafin Twitter domin kai kokenta – Kyakkyawar budurwar mai suna Hafsat Samaila mabai ta roki mabiya shafin a kan su tayata rokon mahaifinta yayi mata aure – Ta kuma bayar da tabbacin cewa za ta zauna koda kuwa auren dole baban nata zai yi mata Wata matashiyar budurwa mai suna Hafsat Samaila tare da shafin Twitter @Oummieeh ta koka a kan gajiya da zaman kadaici babu aure. 

Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta roki mabiya shafin sadarwa ta Twitter a kan su taya ta rokon mahaifinta kan yayi mata aure domin a cewarta a yanzu babu abunda take so sama da hakan.

Hafsat ta kuma jaddada cewa a shirye take tayi zaman aure koda kuma na dole za a yi mata.

Duniya labari: Budurwa ƴar Arewa ta roƙi mahaifin ta yayi mata aure, ko na dole ne Hoto: Twitter/@Oummieeh, Sugar weddings Supply: UGC KU KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai ta yi watsi da neman a tsige Shugaba Buhari Ta wallafa a shafin nata: “Ya ku Ayyuhan nas..dan zaman arxiki da muke a tuwita.. Ku cewa baba na aure nake so..ko na dole ne zan zauna.”

@KabirMtz ya wallafa: “Toh, tunda kin shirya zanzo na biya sadakin aurenki gobe…Indai zaki zauna da kishiya babu matsala to zanzo gaisuwa gobe..” @y_saneey ya ce:-

“Hhhhhhhhh plx duk wacce xaa yiwa mawa auren dole sae ta nemo nii.” @Usman_M_Isah ya ce: “

@sameenuabdoul 

@AlieAbba kune makwafta sai ku taimaka ku isar da Saqo.” 

@FalakinKano ya ce: “In Shaa Allah, zan kira shi a kan haka. Kina ruwa……”  A wani labarin mun ji cewa wata matashiyar budurwa mai shafin Twitter 

@3yesharu ta yi kira ga mazan Hausawa magidanta a kan su duba yiwuwar yin karin aure, cewa yan mata da ke kan layi solar gaji da jira. 

Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta yi kiran ne ga mazan Hausawa da suka yi aure fiye da shekaru biyar da suka gabata. Ta wallafa a shafinta na Twitter: 

“Mazan arewa da suka yi aure tsawon shekaru 5+ ina ganin lokaci yayi da za ku fara kallonmu yan rukunin B. Mun isa a kwashemu amma layin baya tafiya.”

What's On Your Mind?