PDP Reshen Neja Ta Bayyana Zunubin Da Ya Sa Ta Dakatar Da Mu’azu Babangida

0
91

PDP Reshen Neja Ta Bayyana Zunubin Da Ya Sa Ta Dakatar Da Mu’azu Babangida

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa, tsahon gwamnan Jihar Neja, Muazu Babangida Aliyu ya taimaka wa jam’iyyar APC da kudade a zaben shekarar 2015, wanda hakan ya tallafa wajen kayar da jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce saboda wannan dalilin ne aka tabbatar da dakatar da tsohon gwamnan daga jam’iyyar PDP. Haka kuma, jam’iyyar PDP ta maye gurbin Aliyu da Nuhu Zagbayi a matsayin jagoranta a Jihar Neja.
Jaridar Every day Perception ta ruwaiti cewa, jam’iyyar PDP ta reshen Jihar Neja ta tabbatar da cewa Mu’azu Babangida Aliyu yana nan a matsayin wanda aka dakatar da shi. Jam’iyyar PDP ta ce, an dakatar da tsohon gwamna, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu saboda rawan da ya taka wajen juya wa Goodluck Jonathan baya a zaben shekarar 2015. Rahoton ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP ta fito, ta bada wannan sanarwa ta bakin mai magana da yawun bakinta a mazbar tsohon gwamnan, Malam Yahaya Mohammed Usman.Yahaya Mohammed Usman ya ce, suna tare da gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, wanda ya ce Mu’azu Babangida Aliyu yana bin jam’iyyar PDP bashin neman afuwa.

“An wanke mu, mun fada wa ‘yan Nijeriya da mutanen Jihar Neja cewa, Dakta Aliyu ya yaudare mu, ya yi wa jam’iyyar APC aiki.
“Ya yaudari jam’iyyar PDP da shugaban kasa na wancan lokaci, Goodluck Jonathan da dan takarar zabenmu na gwamnan jihar, Alhaji Umar Nasko.” In ji jam’iyyar.
Ya ce: “mun fada cewa ya dauki kudade ya bai wa jam’iyyar hamayya a wancan lokacin a matsayin gudumuwa.”

Yahaya Nasko – Neja Za Ta Samar Da Audugar Da Ba A Yi Tsammani Ba

Kakakin jam’iyyar ya kara da cewa, “mun tabbatar da karin matsayin da aka yi wa Dakta Shem Nuhu Zagbayi a matsayin jagoran jam’iyyar PDP a yankin da Dakta Aliyu ya fito.”

Mai magana da yawun bakin jam’iyyar hamayyar a Neja, bai iya bayar da wata hujja da za ta tabbatar da cewa Dakta Mu’azu Babangida Aliyu ya ba APC kudade a zane shekarar 2015 ba.

Shi dai Dakta Shem Nuhu Zagbayi ya taba rike mukamin mataimakin gwamna a Jihar Neja a lokacin mulkin jam’iyyar PDP.
A kwanakin baya kun ji yadda uwar-jam’iyya ta rusa dakatarwar da aka yi wa jigon jam’iyyar PDP, Muazu Babangida Aliyu saboda laifin yi wa Goodluck Jonathan zagon-kasa. Shugabannin riko na yankin Arewa ta tsakiya photo voltaic yi watsi da matakin da jam’iyyar PDP reshen Jihar Neja ta dauka, suka ce tsohon gwamnan yana cikin ‘yan majalisar BOT na jam’iyyar PDP.

What's On Your Mind?