Osinbajo Ya Zayyana Matakan Gwamnatin Tarayya Na Bunkasa Kimiyya Da Fasaha A Nijeriya

0
106

Osinbajo Ya Zayyana Matakan Gwamnatin Tarayya Na Bunkasa Kimiyya Da Fasaha A Nijeriya

Daga Maigari Abdulrahman,

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce, gwamnati za ta fito da sabbin hanyoyin bunkasa fannin kimiya da fasaha a Nijeriya.

Ya bayyana hakan ne a wurin wani taro da kanfanin manhajar “Google” ya shirya kan shirin kimiya da fasaha a Afrika, a Abuja ranar Alhamis.

Osinbajo, wanda shugaban hukumar bunkasa kimiya da fasaha ya wakilta, Mista Kashifu Inuwa, ya ce Osinbajo ya zayyana matakai da hanyoyin inganta fannin kimiya da fasaha.

Ya ce gwamnatin tarayya na aiki kafada da kafada da masu hannu da shuni domin bayar da shawarwarin matakai har zuwa dabbakawa.

“A kokarin yunkurin sarrafa harkar kasuwanci daidai da zamani, mun yi dokar mallakar biza kai tsaye bayan isowa Nijeriya.

“Hakan na nufin ‘yan kasuwar Afrika za su iya fadada kasuwancinau cikin sauki ta hanyar samun damar shiga Nijeriya ba tare da wata wahala ba.

“Haka kuma, kwamitin masana kan fannin na yukurin fiddo da sabbin shawarwari ga gwamnti kan inganta fannin na kimiya da fasaha da kuma bunkasawa,” in ji shi.

Ta wannan kwamitin, gwamntin Nijeriya na kunkurin samar da tallafin dala miliyan 500 daga babban bankin Afrika domin bunkasa fannin.

A cewar sa, tallafin zai kara taimaka wurin bunkasa hanyoyin gudanrwa da su ka shafi tattalin arzki da kuma gine-gine. Kuma samun nasarar shirin bunkasa fannin a Afrika, ya ta’allaka ne da fasahar kirkira da kuma anfani da na’urar zmanin wurin tafiyar da kasuwanci da masana’antu, kamar yadda yake yanzu a wannan zamanin, in ji shi.

Ya bayyana wannan karnin a matsayin karnin da zo da ababen cigaban rayuwa da kuma saukaka al’amurran yau da kullum ta hanyar anfani da hanyoyin sadarwa na zamani.

To sai dai, mataimakin shugaban kasar ya koka da karancin samun wadannan cigaban a Afrika, inda ya yi kira da a wannan sabuwar marrar cigaban fasaha ta four da za a shiga, ya zama Afrika ta kara yunkurawa yanda ya kamata.

“Alamomi na nuni da cewa, sabon juyin-canjin yanayin masana’antu da tattalin arziki da ke fuskanto mu yanzu, zai ba kananan kasashe damar cike gurbin da ke tsakanin su da manyan kasashe.”

“Wannan sabon juyin kasuwanci da masana’antun, ana iya yinsa daga nesa ba lalle sai ta gangar jiki da jiki ba, sakamakon samuwar kafofin sadarwa da su ke kan mamaye huldar kasuwanci.”

Mataimakin shugaban kasar, ya bayyana cewar, Jihar Legas ce da mafi samun nasara a nahiyar Afrika a wannan fannin.

Ko a 2019, Nijeriya ta samar da ofishin tsarawa da kuma bunkasa fannin kimiya da kasuwanci domin sauya tattalin arizki da kasuwancin Nijeriya da ya doru kan kimiya da fasaha, in ji shi.

Ta hanyar samar da ofishin NITDA din, gwamnatin Nijeriya ta iya samar da hanyoyin bunkasa fannin kasuwanci da kirikira, tare da sauya harkar kasuwanci a kasar, a bayanin nasa.

What's On Your Mind?