Osinbajo Ya Nemi Amurka Ta Taimaka Wajen Samar Da Riga-kafin Korona

0
83

Osinbajo Ya Nemi Amurka Ta Taimaka Wajen Samar Da Riga-kafin Korona

Mataimakin Shugaban kasa  Farfesa Yemi Osinbajo ya yi mkira da kasar Amurka da ta goyi bayan kiran da ake yi na maganar adalci, musamman ga sauyin al’amuran yanayi yadda ake samun iska mai gurbata muhalli, kuma ya yi kira da ayi jagoranci wajen kokarin tabbatar da samun sauki ga allurar rigakafin COBID-19 ga kowacce kasa.

Mataimakin shugaban kasar har ila yau kuma ya yi kira da Amurka da ta sake tsara manufofinta na kasashen waje tare da nahiyar Afirka, ta yadda za a bunkasa ci gaban tattalin arziki, kara tsaro da  kuma inganta al’amuran da suka shafi shugabanci.

Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande a wata sanarwa daya fitar ranar Litinin a Abuja ya bayyana cewa, mataimakin shugaban kasar ya gabatar da shi jawabin ne a kusa da ayi  taron na 207 Johns Hopkins na Jami’ar nazarin Afirka.

Taken taron dai shi ne “Sake Hadin gwiwar Amurka da Afirka: Sabon tsarin manufofin kasashen waje”, an shirya shi taron ne daga makarantar kwalejin nazarin al’muran kasa da kasa (SAIS).

Ya ci gaba da cewar “Ya kamata Amurka da Afirka suyi aiki tare don yakar canjin yanayi da dumamar yanayi mai matsakaici, tare da sauya makamashi daga burbushin halittu zuwa makamashi masu sabuntawa.

“Kasashen Afirka solar himmatu kwarai recreation da shi wannan  al’amari na aiwatar da manufofin yarjejeniyar Paris kan canjin yanayi.

“Dangane da sadaukarwar da aka dade ana yi recreation da gurbataccen hayakin sifiri nan da shekara ta 2050, akwai karuwar halayyar cibiyoyin hada-hadar kudi na ci gaba da ficewa daga sa hannun jari a cikin harkar mai.”

A cewar sa, wannan ya hada da shawarar da Bankin duniya ya yanke ta dakatar da bayar da kudaden tallafi na mai da kuma iskar gasoline.

Har ila yau ya kara jaddada“Kuma sababin hane-hane kan samar da kudade ga ci gaban iskar gasoline a yanzu haka, ita kungiyar tarayyar Turai, da Burtaniya Eire ta Arewa da kuma Amurka suna la’akari da shi.

“Yayin da ake da kyakkyawar niyya, shi wannan yunkurin ya kasa yin la’akari da ka’idojin aiki na bai daya, amma ya bambanta kuma ba wanda ya bari a baya, wadanda aka sa su cikin yarjeniyoyin duniya, kan ci gaba mai dorewa da aikin sauyin yanayi.

“Wajibi ne Amurka ta yi dukkan abubuwan da suka kamata don kawo karshen wannan mummunar dabi’ar da za ta kawo nakasu, ga fahimtar nauyin da ke kanmu baki daya, kan magance sauyin yanayi; abin da ake bukata shi ne sauyi mai adalci wanda kowa yake bukatar samu da kum haduwa da shi. ”

Kwanan nan Osinbajo ya yi kira da a sauya al’amura zuwa ganin adalci ya dauwama, musamman kiran da ya yi ga hukumomi, da kasashen yammaci da su dakatar da dage kudaden da aka shirya wa kasashe masu tasowa.

Mataimakin Shugaban ya yaba wa Amurka don taimakawa wajen inganta sakamakon kiwon lafiya a Afirka, ciki har da shirin Shugaban kasa na gaggawa recreation da cutar kanjamau (PEPFAR).

Ya yi kira da yin irin wannan al’amari na hadin gwiwa,  dangane da samar da allurar rigakafin cutar Korona a kasashen Afirka.

“Ita dai annobar Korona ta nuna bukatar daidaita ayyukan don samun damar bunkasa yadda ake yaki da annobar,  yayin da kuma ake kara inganta kayaayyakin kula da kiwon lafiyar al’umma a kasashe masu tasowa da kuma wadanda suka bambanta a al’amarin na tunkarar hanyar ta ci gaba.

“Yanzu ba lokacin ba ne recreation da allurar rigakafin cutar da kuma hana fitarwa zuwa kasashen waje, a maimakon haka za a yi aiki tare ne don yin allurar rigakafin cutar gaba daya.

“Amurka na iya jagorantar kokarin tabbatar da cewa dukkan kasashe da jama’arsu za su iya samun damar yin allurar rigakafin, ba tare da la’akari da albarkatun da suke da su ba kamar yadda ya ce”.

A cewar Osinbajo, ya kamata a inganta hadin gwiwar da ke tsakanin nahiyar da inganta hadin gwiwar da ke kawo ci gaban tattalin arziki, kara matakan tsaro, yaki da cututtuka, inganta shugabanci da kuma magance sauyin yanayi.

Ya ce Afirka ta fuskoki masu yawa wata dama ce ta samun  bunkasar tattalin arzikinta, kasancewar tana da karfin da za ta iya zama ginshikin ci gaban kanta.

“Hakika, kamar yadda sauran bangarorin duniya ke kallon ta, Afirka na tafiya da karfin gwiwa don hada tattalin arzikinta ta hanyar wani tsari na shekarar 2063 mai akidar kirkirar Tarayyar Afirka. kasuwancin nahiyar Afirka (AfCFTA).

Kasar Amurka tana da kyakkyawan matsayi don jagorantar huldar kasuwanci da sa jari da Afirka. Kuma tana da kyakkyawar dangantaka da dokar ci gaban Afirka da bada damar yin hakan (AGOA).

“Dokar, wacce ta cire dukkan haraji kan kayayyaki 6,400 da ake da su don fitarwa zuwa Amurka, ta baiwa wasu kasashen na nahiyar Afirka damar cin gajiyar hakan.”

Dangane kuma da inganta tallafin da Amurka ke bayarwa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel, Osinbajo ya ce  da akwai bukatar a kara kaimi wajen kawo karshen mulkin ta’addanci a  shi yankin wani al;’amari ne daya dace ya zama abin so ne.

Ya ce duk da cewa a bayyane yake cewa barazanar kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na karuwa, amma za a ga cewar Kwamandan Afirka na Amurka tun daga shekarar 2020, ya sauya daga dabarun lalata kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a Afirka ta yamma don kawai hana yaduwar su.

“Karuwar hare-hare da hada karfi da karfe da aka samar tsakanin wadannan kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, suna kira da a sake duba shi wannan matsayin.

“Wataƙila yanzu ne lokacin da za a iya yin tsoma baki sosai recreation da ayyukan da Amurka ke tallafawa, don kawar da ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya a gabas ta tsakiya kamar dai yadda ya ce”.

Mataimakin shugaban kasar ya ba da shawarar cewa dangantakar da ke tsakanin Amurka da nahiyar Afirka bai kamata ta kasance ta bangare daya kadai ba.

A baya, wadanda suka shirya taron solar yaba wa mataimakin shugaban kasar kan jagoranci da jajircewa.

Farfesa Elliot Cohen, shugaban makarantar sakandaren karatun digiri na kasa da kasa na kwalejin, ya ce, ya yi matukar farin ciki da Farfesa ya tashi har ya kasance a matsayin mataimakin shugaban kasa.

What's On Your Mind?