Osinbajo Ba Shi Da Sha’awar Takara A Zaben 2023 – Fadar Shugaban kasa

- Advertisement -

Osinbajo Ba Shi Da Sha’awar Takara A Zaben 2023 – Fadar Shugaban kasa

Daga Mahdi M. Muhammad,

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo (SAN) ba ya nuna sha’awar takara a yakin neman zabe na zaben shugaban kasa na shekarar 2023.

A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ofishin mataimakin shugaban kasar, Mista Laolu Akande, ya ce, Osinbajo ba yi da wata alaka da yakin neman zaben ko kuma kungiyar da ke daukar nauyin sa.

Fadar Shugaban kasa ta bayyana kamfen din a matsayin wani abin da zai dauke hankalinsa, duk da cewa ta bayyana cewa Osinbajo bai bayyana wata aniya ta tsayawa takarar shugabancin kasar a 2023 ba.

“An ja hankalin Ofishin Mataimakin Shugaban kasa zuwa wani shafin yanar gizo (supportosinbajo.ng) da ke kira ga ‘yan Nijeriya da su shiga kungiyar sa kai da ke tattara goyon baya ga Farfesa Yemi Osinbajo (SAN), gabanin zaben shugaban kasa na 2023,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Cikakkun bayanai na wannan rukunin yanar gizon da rokon kungiyar a halin yanzu suna ta yadowa a manjahar WhatsApp tare da shawarar cewa Farfesa Osinbajo a hankali zai bayyana sha’awarsa a zaben 2023.”

“Ofishin mataimakin shugaban kasa ba shi da wata alaka da wannan rukunin yanar gizon ko kungiyar da ke bayansa, kuma yana daukar irin wannan tallar a matsayin wani shagala da ba dole ba,” in ji sanarwar

- Advertisement -