Oshoala Ta Zama ‘Yar Afrika Ta farko Da Ta Lashe Kofin Zakarun Turai Na Mata

- Advertisement -

Oshoala Ta Zama ‘Yar Afrika Ta farko Da Ta Lashe Kofin Zakarun Turai Na Mata

Shahararriyar ‘yan wasan kwallon kafar nan ta mata, Asisat Oshoala ta kafa babban tarihin zama ‘yar Afrika kuma ‘yar Nijeriya mace ta farko da ta lashe kofin gasar Zakarun Turai ajin mata.

Shahararriyar ‘yar wasan mai shekaru 26 a duniya, ta shiga wasan karshen da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a gasar Zakarun Turan ne a mintuna na 71, wasan da daga karshe suka lallasa kungiyar ta Chelsea da kwallaye Four-Zero.

Tawagar Barcelona ajin mata ta samu nasarar ce ta hannun ‘yan wasanta Melanie Leupolz, Aleia Puttellas, Aitana Bonmati da Caroline Graham, ya yin da ‘yar Najeriya Azizat Oshoala ta jefa ta biyar amma alkalin wasa ya soke ta bisa hujjar tayi satar shiga gida.

Kafin nasarar bana, yunkurin karshe da Barcelona ta yi wajen lashe kofin gasar zakarun Turan ajin mata, shi ne wasan da Lyon ta lallasa ta da kwallaye Four-1, wasan da yaja cece-kuce a kungiyar ta Barcelona.

- Advertisement -